MATA KUYI HATTARA DA BINCIKEN WAYAR 📱 MAZAJENKU
https://chat.whatsapp.com/LRPQDrs7qSoKXuSspoPkFm
*TAMBAYA*❓
Assalamu Allaikum mallam ya kokari Allah ya taimaka Ameen tambaya ce Wata mata ce suna zaune da mijinta lfy tana matukar sonshi kuma tana yi mishi biyayya iya gwargwado asalima bashi da abinyi buga buga yakeyi fadi tashi tana zaune dashi lfy harkimanin shekara biyar duk wannan tsawan lokacin baya San tana taba mishi waya duk runtsi bazai cire password agabanta ba ta kyalishi ahakan amma abin yana damunta saita lura yana dadewa baiyi bacci ba kuma ko wanka zashi da wayar yake tafiya ,watarana by mistake sai ya manta da wayan baifita da itaba kuma wayar abude ya barta saboda screen din ya samu matsala shine tayi amfani da wannan daman taga wai meyake boyemata ashe soyayya yake yi da zaurawa kuma ba karamin hidima yake musu ba kuma suna turo mai da hotuna sanye da kananan kaya ajikinsu tunda ga ranan ta tsane shi kuma bama ta son ganin shi saboda a hakama baya iya kauda kai akan mata ballantana yasamu abinyi sai Allah shine take son abata shawara mallam nagode
*AMSA*👇
Wa Alaikis Salaam:- toh a Gaskiya ita Wannan Matar tayi Kuskure sosai, Kuskuren ta Shine bai kamata ta Rika Sanya ido akan Abunda Mijin yake yi musamman ta Rika Binciken Wayar sa Domin ta ga Menene ake yi ba. Ita ne yakamata ya sanya ido a kanta domin tana Karkashin Kulawar sa ne hakkin ta na Kanshi na Kula da duk wani Motsin ta, amma bawai ita ne Zata Sanya ido a Kansa wanda Kullum ita damuwan ta ta ga Menene yake yi da wayar Sa a Kullum ba.
Allah Swt da Annabi Sallallahu Alaihin Wasallam suna Ce mana Shi yin Zato Zunubi ne koda Kuwa ya Kasance Wannan abun Gaskiya ne. Toh yanzu da tayi ta yin Binciken har dai Allah ya Nuna mata Wannan, Shin menene ta Janyowa Kanta? Ba ta janyowa kanta wani damuwar da ita bata yi sammanin sa nan kusa ba alhalin tana zaune lafiyar ta qlau? Sannan menene Amfanin Abunda tayi? Tana Zaune Lafiya-Lafiya dashi toh gashi Yanzu tana Fushi dashi har ta tsane Shi Shin menene Binciken ta ya Haifar mata? Shin Abunda yake yin ya dena shi ne da ta gane hakan? Haba Mata meyasa kuke yin haka? Yin Zargi Haramun ne a Addinin Musulunci meyasa kuke Zargin Mazan ku?
Wajibi ne gare ku Matan Aure kuyi Hattara da Binciken HANDSET na Mazajen Ku, idan ba Ku dena ba Babu Shakka Wata rana Za ki iya Binciko Abunda Zai yi Sanadin Ki har Lahira. Bai Kamata Ace Kina tare da Mijin ki Ace yace
Miki baya Son ki Rika taɓa Wayar Sa kuma kina ganin Sa Kullum baya ajiyewa inda za ki gani ki ɗauka, kuma Kullum wayar tana Cikin Password, Kuma Ki ce dole-dole sai Kin Matsa da Bincike kin san menene a Cikin Wayar sa? Yake yi dashi a Cikin dare? Ina Ruwan ki? Me yayi Zafi haka? Ina ruwan ki dashi ta Wannan Ɓangaren Qabarin ki ɗaya ne dashi?
A Gaskiya irin Wannan Ɗabi'ar na Binciken Wayar Miji baya Kan Tsari na Koyar Addinin Ku, Don Haka Wajibi ne Ku Ji tsoron Allah ku ɗena yin haka, Idan Kina Binciken Cewar yana neman Zaurawa a Waje ne yana Kashe Musu Kuɗi ina Ruwan ki? Ko buga buga yake babu Ruwan ki da abunda yake yiwa wasu a waje indai yana miki kema, Shin Mata nawa ne Allah yace yayi? Kina Fushi da Allah ne ko Kuma da Mijin ki? Shin idan Zai Kara Auren Za ki iya Hana shi ne duk da Binciken naki? Meyasa kuke son hana Abunda Allah ya Halatta ayi shi? Saboda Haka ku ɗena irin Wannan domin ba Zamantakewar Aure mai Ƙyau bane. Idan Misalin Mijin yana Fita waje yana Neman Matan Banza yana Zina da su, nan ne yakamata idan Kin tabbatar kin gani da idon ki Kiyi Fushi dashi ki tsane shi domin ya Saɓawa Ubanjigin ki, Sannan Zinan da yake yi Zai iya Ɗauko Ciwo ya Sanya miki, toh nan ne Zaki nemi Hanyar Rabu dashi ko ya Chanja Halin sa Domin kada ya Ɗauko Ciwo ya Saka miki. Toh amma wata Kila ba Zina yake yi ba, iya Abunda kika faɗa shi yake yi, kenan Wannan bai kamata Ace Mace ta tsani Mijin ta har ta yi Fushi dashi ko ta Ƙi yi masa biyayya ko Sauke Hakkin Aure ba.
Don haka, Shawarar da Zan bata Shine, tayi Hakuri da abunda ta gani ya riga da ya Wuce amma ta Kiyaye gaba, tayi Hakuri Fushi, da Tsanan Mijin ta da tayi ta ji tsoron Allah ta Sauko daga Wannan Fushin nata Sannan ta Sanya Son Mijin ta a Ranta kamar DA can bata da wani ya Wuce Shi ɗin Shine Hanyar Shigar ta Aljannah hakanan shima Mijin, kada ta ce wai Don ta ga Wannan abun tace ita zata yi Fushi da Mijin ta ta ji ta tsane shi ta Ƙi yi masa biyayya ko biya masa Hakkin sa, Matukar zata yi haka toh ta Sani Cewa tana Cikin Fushin Allah da na Mala'ikun Sa. Abunda ta gani ma ita nata Nafila ne, inda wata zata gaya miki abunda ta gani a wayar Mijin ta, da ke za ki ce ba ki ga Komai ba. Kuma hakan bai hana zama da Mijin ta ba, kuma bata tsane shi ba. Don haka itama kada tayi hakan tayi Hakuri.
Abunda yakamata tayi Shine ba Fushi da tsanan mijin ta zata yi ba, ai ita Matar sa ne sai ta bi shi ta Hanyar da Addinin ta yace wajen Janyo Hankalin sa Zuwa gare ta, ta bi duk Wani Hanyar da Shari'a ya tana da wajen Ceto Mijin ta daga Abunda ta gani har ya sakata fushi dashi ta ji ta tsane shi. Tayi ta Samu Lada Biyu. Amma bata yi ba Sai ɗiban Laifi kuma take yi.
Idan tayi Haka in mai gyaruwa ne Mijin, sai ya gyaru ya Chanja duk Wani Rayuwar sa, idan Kuma ba Mai Gyaruwa bane sai ta Ci gaba da Hakuri dashi da Juriya har Allah ya kawo mata Mafita. Amma tayi Bincike ta tarar da Abunda bata son gani Ranta ya Ɓaci ta ji ta tsani Mijin ta, Maimakon ta sanya Natsuwa a Ransa itama ta Ƙwantar da Hankalin ta sai tace A'a. Shin idan ma Mijin yana da Niyyar bari sai ya ga tayi hakan shin Zai bari ne ko Zai kara yi ne? Ke Matar sa ne da me Matan Wajen suka fi ki? Ace ba Za ki yi iya Kokarin ki wajen ganin Kin Ceto shi ba? Sai kuma Ace kene Za ki tsane shi waye zai so shi toh? Don kin ga wani aibu a tare dashi. Shekara nawa kuna zaune yaran ku nawa ne duk Wannan bai ishe ki ba, sai kin janyowa kanki Masifa kuma?
Shin yanzu idan ta Matsa Mijin ya Sake ta, tayi gaba ne ko tayi baya? Nasara tayi ko Rashin Nasara? Shin menene Binciken nata ya jawo mata? Idan Auren ne sai ya Auro wanda ta ganin, ita kuma ya Sake ta, ya Auro wata su zo suna More Rayuwar su ke Kuma kina gidan Ku, an bar ki da Ciwon Kirki da Hawan Jini. Shin waye ya jawo miki Wannan? Kene. Saboda Haka ina bata Shawarar da tayi Hakuri duk Wannan abun ya wuce, idan tana Fushi da Mijin ta ko Mijin yana Fushi da ita dalilin Wannan, tayi Hakuri ta same shi ta ba shi Hakuri ya Hakura sannan tayi Alkawarin ba zata sake yin Hakan ba insha Allahu. Shikenan su kuma Zaman Auren su kamar da Cikin Ƙwanciyar Hankali.
Idan Kuma ta ce A'a, zata ci gaba da Fushi dashi da tsanan Shi, toh Gaskiya zata Wahala kuma ba zata yi Nasara ba. Sannan don Allah Mata idan har Mijin ki baya Son ki Rika taɓa Wayar Sa kin Fahimci Cewar Lallai ne baya Son hakan, toh fah Ki ji Tsoron Allah ki Ji Tsoron Mutuwar ki, kada Kice Zata Ki Tsananta Bincike Kice Dole-dole Sai kin san meyasa baya Son ki ga Wayar sa Kuma kina Matsayin Matar sa. Wallahi idan Kin matsa Za ki iya gano Abunda Zai yi Sanadin Rayuwar ki. Don Haka Mata a Kiyaye. Amma idan Mijin ki ya Ba ki Damar Taɓa Wayar sa komai kina yi Shikenan. Amma idan bai ba ki ba. Toh babu Ruwan ki da Wayar sa. Dafatan ta Fahimta???
Wallahu A'alamu.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: ▽_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*