YADDA AKE YIN ISTIKHARA A SUNNAH
https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA
*TAMBAYA*❓
Assalama alaikum wsragamatullah
Dn allah malam yaya akeyin istahara
*AMSA*👇
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu
An kar6o hadith daga Jabir ibn Abdullah, Allah ya yarda dashi yace:
Manzon Allah (SAW) ya kasance yana koya
mana yin Istikhara (neman zabin Allah) a cikin dukkanin al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga cikin surorin Alqur'ani.
Ya kance damu:
Idan dayanku yayi niyyar yin wani al'amari to yayi sallah raka'a biyu ba farillah ba sannan yace:
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﺳﺘﺨﻴﺮﻙ ﺑﻌﻠﻤﻚ
ﻭﺃﺳﺘﻘﺪﺭﻙ ﺑﻘﺪﺭﺗﻚﻭﺃﺳﺄﻟﻚ ﻣﻦ ﻓﻀﻠﻚ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢﻓﺈﻧﻚ
ﺗﻘﺪﺭ ﻭﻻﺃﻗﺪﺭﻭﺗﻌﻠﻢ ﻭﻻ ﺃﻋﻠﻢ ﻭﺃﻧﺖ ﻋﻼﻡ ﺍﻟﻐﻴﻮﺏﺍﻟﻠﻬﻢ
ﺇﻥ ﻛﻨﺖ ﺗﻌﻠﻢ ﺃﻥﻫﺬﺍ ﺍﻷﻣﺮ ( ﻭﻳﺴﻤﻲﺣﺎﺟﺘﻪ ) ﺧﻴﺮ ﻟﻲ
ﻓﻲﺩﻳﻨﻲ ﻭﻣﻌﺎﺷﻲ ﻭﻋﺎﻗﺒﺔﺃﻣﺮﻱﻓﺎﻗﺪﺭﻩ ﻟﻲ
ﻭﻳﺴﺮﻩ ﻟﻲ ﺛﻢ ﺑﺎﺭﻙ ﻟﻲ ﻓﻴﻪﻭﺇﻥ ﻛﻨﺖ ﺗﻌﻠﻢ ﺃﻥ ﻫﺬﺍ
ﺍﻷﻣﺮﺷﺮ ﻟﻲ ﻓﻲ ﺩﻳﻨﻲ ﻭﻣﻌﺎﺷﻲ ﻭﻋﺎﻗﺒﺔ ﺃﻣﺮﻱﻓﺎﺻﺮﻓﻪ
ﻋﻨﻲ ﻭﺍﺻﺮﻓﻨﻲ ﻋﻨﻪ ﻭﺍﻗﺪﺭ ﻟﻲ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﺛﻢ ﺭﺿﻨﻲ ﺑﻪ .
ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻋﻦ ﺟﺎﺑﺮ ﻣﺮﻓﻮﻋﺎ .
Allahumma inna astakhiruka bi ilmika, wa'as taqdruka bi qudratika wa as'aluku min fadhlika azim fa innaka taqdiru wala aqadiru, wa ta,alamu wala a'alamu, wa anta allamul guyubi.
Allahumma in kunta ta'alamu anna hazal amri
--------- khairuli fi dinni wa ma'ashi wa aqibati
amri fa qadirhuli wa yassirhuli summa barikli fihi, wa in kunta ta,alamu anna haza amri sharrun li fi dinni wa ma'ashi wa aqibati amri fa sarrifni anhu wa sarifni anhu wa qadurli khairan haisu kana summa arzini bihi.
Ya Ubangijina! ina neman zabinka da iliminKa, ina neman tabbatuwar ikonKa, ina rokan falalarKa Mai girma.
Kai keda iko ni bani dashi, Kaine Masani ni ban san (komai ba) Kaine masanin abin da yake boye.
Ya Ubangiji na! In kana ganin wannan abu kaza (sai ya fadi abin da yake istiharan a kai) shi yafimin a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, to ka tabbatar min dashi, ka sauqaqe min sannan kayi min albarka a cikinsa.
In kuwa kana ganin wannan abu sharrine gare ni da addinina da rayuwata da qarshen lamarina, ka juyar dashi daga gare ni, nima ka juyar dani daga gareshi, ka qudurtarmin da
alkhairi sannan ka amintar min dashi"
[Bukhari].
Duk wanda ya nemi zabin Mahalicci, kuma
yayi shawara da talikai muminai, kuma yayi
azama a cikin lamarinsa, to bazai yi nadama ba Insha Allah.
Domin Allah Madaukakin Sarki yace:
"Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka quduri aniya, toka dogara ga Allah.
Ba mafarki ake yiba kamar yadda mutane da yawa suka dauka. Ana ganewa ne da yanayin nutsuwar zuciya, idan aure ne sai kaji zuciyarka ta qara nutsuwa da yarinyar, idan
sana'ace kakeso kafara sai kaji zuciyarka ta nutsu da sana'ar kuma hanyoyin aiwatarwa sun kara yi ma ka sauki.
Idan kuma babu alkhayri za ka ji abun ya fita daga ran ka.
Allah Ta'ala yayi mana za6i mafi alkhairi a dukkan lamuran mu.
WALLAHU A'ALAM
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: ▽_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*