SOYAYYA A SOCIAL MEDIA (YANAR GIZO)



SOYAYYA A SOCIAL MEDIA (YANAR GIZO) 

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

*TAMBAYA*❓

Assalamualaikum malam,yagida ya kokari damu.Allah ya saka da alkhairy,Amin
Malam nine wani kesona kuma a online muka hadu yana karatu a qasar waje,saiya kasance Allah ya hada jinina da nashi,nidai gsky bantaba sashi a rainaba a matsayin masoyi amma shi yaa damu dani sosai,saita kasance har alheri yana turomin kuma ina amsa,sannan yaci burin inya dawo shida aure yake sona amma ni malam bantaba ganinsabaa soyayyan online ne kawai
Tambayata anan shine duk abinda yake bani banike rokansaba amma inya bani ina amsa amma nifa bawai sonsa nakeba sbd bantaba ganinsabaa,karban abubuwanda nakeyi inada laifi?
Na biyu malam idan ya dawo muka hadu naga yamin zan iya auransa,amma kaga bawai muntaba haduwa bane kuma kasan so gamo na jini ta iya yuwuwa nagansa a zahiri naji be kwantaminba,kuma kaga ai mutum baxe aura Wanda zuciyansa bata natsuba,idan naki amincewa dashi bayan mun hadu in beminba hakan yaudarace? 
Nagode Allah ya saka da alkhairy.


 *AMSA* 👇

1. Na farko dai Bai Kamata Ki Na Karbar Kudinsa ba. Sabida Karbar kudinsa ba da Niyyar Aurensa ba, wannan Kai Tsaye Haramun ne. Kuma Yaudara Ce. Sannan yin Hakan Gaskiya Zalunci Ne. Kuma zaki Biya shi Ko da a gaban Allah Ne.
2. Abu na Biyu Shine. Idan kin ganshi kuma Baiyi Miki ba. To Wannan Kam Babu wani Abu. Sabida a Musulunci An Baiwa Mutum Zabi Akan Wanda yake son ya Aura. Mqce ko Namiji. Haka zalika, Itama mace sai wanda take so zata Aura. Ma'ana sai wanda ya kwantawa a Ranta Zata Aura. Sabida haka Mutum zai Aura Wanda yayi Masa ne Kawai.
  Idan haka ne to fa hakan ba zai Zama Yaudara ba. Amma dai da za'a ce kin ganshi kuma kikayi ta cin kudinsa Alhalin ba zaki Aure shi ba. To kin karbi haramun da Hannunki. 
 Sannan me zai hana ya turo Miki hotunnsa Tinda akwai social media. Haka zalika Me zai hana kuke yin Vedio Call yadda zakike ganinsa yana Ganinki.?
 Sannan ae zai Iya Yimiki Vedio din Kansa da Kansa ki ganshi ba? Ga hanyoyi Nan Barkatai da zaki ganshi babu Adadi.
 Banki ko idan bayan Kun Hadu ba kuma kika Fahimci cewar bashi da Kyakykawan Hali ko bashi da Kyakykawan Mu'amula. To na Yarda da wannan. Amma haka Kawai kike karbar kudin bawan Allah da Niyyar Zaki Aure Shi. Alhalin Kuma kina da Wanda zai Aureki, Wannan Zalunci ne.
 Sabida haka Kenan, Idan kina son ki Hadu da Allah Salin-alin sai kin Biya shi duk Abinda kika karba daga Hannunsa. Sai dai ko idan shine ya Yafe Miki. Sabida da yawa Mata Suna Ganin Kamar Sun ci Banza. Nan Kuwa ba haka Abin yake ba. Indai kika Karbi wani Abu na wani da Niyyar zaki Aure, shima kuma ya baki wannan Abin da Niyyar zai Aureki. Alhalin ke ba haka Abin yake a wajen ki ba. To fa Akwai Ranar Sakamako.

Allah shine Masani.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)