TA TSUFA SHIN ZA'A IYA YI MATA ALWALA?!
https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT
*TAMBAYA*❓
Assalamu alaikum.
Malam Muna da kaka tsohuwa wajen shekararta 90, gaskiya ta koma kamar jaririya, wani lokacin tana gane mutane wani lokacin bata ganewa, gashi bata son sanyi ko ruwan dumi ne, ya za'ayi da ita za'a dinga yi mata alwala tayi sallah?
*AMSA*👇
وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،
Idan mutum ya tsufa sosai ta yadda har ya kai ga rudewa baya gane mutane kuma baya gane lokacin sallah, a takaice dai hankalinsa ya samu tawaya sosai. Toh wannan tsoho ko tsohuwa sallah ba wajibi bace akan sa.
Amma idan ya dawo haiyacinsa a wani lokaci, toh ya shiga sahun mukallafai. Saboda haka zaiyi ibada alokacin da yake cikin hankalinsa.
ﻭﻗﺪ ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: (ﺭُﻓِﻊَ ﺍﻟْﻘَﻠَﻢُ ﻋَﻦْ ﺛَﻠَﺎﺛَﺔٍ: ﻋَﻦْ ﺍﻟﻨَّﺎﺋِﻢِ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﺴْﺘَﻴْﻘِﻆَ، ﻭَﻋَﻦْ ﺍﻟﺼَّﺒِﻲِّ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﺤْﺘَﻠِﻢَ، ﻭَﻋَﻦْ ﺍﻟْﻤَﺠْﻨُﻮﻥِ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﻌْﻘِﻞَ) ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ (4403) ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ (1423) ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ (3432) ﻭﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ (2041) ﻗَﺎﻝَ ﺃَﺑُﻮ ﺩَﺍﻭُﺩ: ﺭَﻭَﺍﻩُ ﺍﺑْﻦُ ﺟُﺮَﻳْﺞٍ ﻋَﻦْ ﺍﻟْﻘَﺎﺳِﻢِ ﺑْﻦِ ﻳَﺰِﻳﺪَ ﻋَﻦْ ﻋَﻠِﻲٍّ ﺭَﺿِﻲَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻨْﻪُ ﻋَﻦْ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲِّ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﺯَﺍﺩَ ﻓِﻴﻪِ: (ﻭَﺍﻟْﺨَﺮِﻑِ). ﻭﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ
_Haqiqa *Annabi (Sallallahu alaihi wa sallam)* yace: An dauke alqalami daga (mutane) uku, daga (mutum) mai barci har sai ya farka, daga yaro har sai ya girma, daga mahaukaci har sai ya dawo a hankalinsa._
_*(Abu Dawud, 4403), (Tirmizi, 1423), (An-nasaa'i 3432) da (Ibn Majah, 2041).*_
*Abu Dawuda* yace: An ruwaito daga *Ibn Jurayj* daga *Qasim ibn Yazid* daga *Ali (radiyallahu anhu)* daga _*Annabi (sallallahu alaihi wa sallam)*_ sai ya kara (da cewa) _"da wanda ya rude (saboda tsufansa)"._
_*Albaani ya inganta wannan hadisi a SAHIH ABI DAAWUDA.*_
Anan kalmar الخرف yana nufin mutum Wanda ya samu rudewa saboda tsufan sa.
An ambata acikin _*Awnil Ma'abud*_ aka da'ifantar da ruwayar da ta ambata "والخرف" saboda isnaadin sa. Saidai wani abu da yake nuna ingancin ma'anar sa, wanda *As-subki* ya ruwaito.
*As-subki* yace: za'a iya sanya الخرف acikin wadancan mutane uku da aka dauke musu alqalami, kuma ya inganta. Abinda ake nufi anan shine mutum wanda ya tsufa har ya rasa hankalin sa saboda yawan shekarunsa. Tsoho yana iya rudewa ta yadda bazai iya gane ababe ba. Wanda hakan yake fitar dashi daga sahun mukallafai. Kuma ba'a kira shi *Mahaukaci* ba, domin shi mahaukaci yana iya warkewa ya dawo hankalinsa, amma shi rudadden tsoho sabanin haka ne. Shiyasa acikin hadisi ba'a ce حتى يعقل ba. Saboda a mafi yawan lokuta rudadden tsoho baya warkewa har mutuwar sa. Amma idan ya dawo haiyacinsa a wani lokaci, toh ya shiga sahun mukallafai.
Saboda haka wannan tsohuwa idan tana cikin hankalinta tana gane kowa da komai toh kuyi mata alwala da ruwan da bazai cutar da ita ba sai tayi sallah, idan babu ruwan da zai dace da lafiyarta, toh sai kuyi mata taimama tayi sallah.
Amma idan ta shiga rudewa ta yadda bata gane lokaci da mutane, toh anan an dauke mata sallah.
والله أعلم،
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.