YADDA SUNNAH TA KOYAR GAME DA MAI FAMA DA JINNU, DA YADDA ZA A KARE KAI KAFIN FITINUWA DASU.
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds
*TAMBAYA* :❓
Assalamu alaikum. Tambayata Ita ce: Yaya Sunnah ta koyar ga wanda jinnu ke damu, da kuma kariya daga su ko da ba suna jikin Dan Adam ba ne?
*AMSA* :👇
Wa'alaikumus Salam, ƴar uwa game da wanda ke fama da jinnu, ya tabbata za a iya yi masa ruq'ya wadda ba ta saɓa wa Shari'a ba, saboda hadisin Aufu bin Malik Al'ashja'iy da ya ce: Mun kasance muna yin ruqa a zamanin jahiliyya, sai muka ce; ya Manzon Allah mene kake gani game da hakan? Sai Manzon Allah ya ce: " Ku nuna min ruqan naku, babu laifi ga ruqa matuqar babu shirka a cikinta".
Sahihu Muslim 2200.
Wannan ya zama dalili a kan yin ruq'ya matuqar an kaucewa shirka a cikinsa. Ibn Hajar ya ce:
"Haqiqa malamai sun yi ijma'i a kan halascin yin ruq'ya idan an kiyaye sharuɗɗa guda uku, ya zama da maganar Allah SWT za a yi, ko da sunayensa da siffofinsa, ya zama da harshen Larabci za a yi, ko kuma wani harshen da aka san ma'anarsa, ya zama an qudurce a zuci cewa ita ruq'ya ba ita ce take tasiri da kanta ba, tana yin tasiri ne da nufin Allah SWT.
Duba FAT'HUL BÁRIY (10/227).
Shi ma Shaikhul Islam Ibn Taimiyya ya faɗa cewa: "Malaman Musulunci sun hana yin ruq'yar da ba a fahimtar ma'anarta, saboda ita ce matattarar shirka, ko da kuwa mai yin ruq'ya ɗin bai san ita shirka ba ce".
Duba littafin AKHBÁRUL JINNI WASSHAYAƊEEN shafi na 21, na Ibn Taimiyya.
Wato dai dole mai son yin ruq'ya ya yi ta da maganganun Allah, da sunayensa da siffofinsa, kuma ba a so a yi ruq'ya da kalmomin da ba a san ma'anarsu ba, haka kuma ba a son mutum ya riqa tunanin cewa ita ruq'yar ce za ta samar da waraka da kanta, wato a qudurce cewa Allah ne zai ba da lafiya.
YADDA ZA A NEMI KARIYA DAGA ALJANU
Yana daga cikin hanyar samun kariya daga jinnu: kiyaye farillai da wajibai, da nisantar haramtattun al'amura, da yawan tuba daga dukkan munanan ayyuka, da yawan kyautata yin zikirori da addu'o'i, da isti'azozi da shari'a ta yarda da su.
Duba Addu'a'u Minal Kitábi Wassunnah, Wal 'iláju Birruqa Minal Kitábi Wassunnah, shafi na 112.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕