WAI AKWAI ADDU'AR DA AKE YI MA YARA MATA DON KARIYA DAGA ZINA?



WAI AKWAI ADDU'AR DA AKE YI MA YARA MATA DON KARIYA DAGA ZINA?

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum 
Malam barka da warhaka, Allah yaqarawa malam lafiya da istiqaama akan tafarkin sunnah. 
  Malam wasu É—alibai sun tambayeni cewa wani malami ya faÉ—i musu cewa "akwai wata addau'ah da ake karantawa atofa afarjin yara mata jarirai domin karesu daga zina idan sun girma " malam menene ingancin wannan maganar, idan kuma bata inganta ba akwai wata addu'a daban da ake karantawa domin nima ma yara kariya daga zina!!?

*AMSA*👇

Wa'alaykumussalam
 Babu wannan addu'ar cikin Alkur'ani babu a sunnah tsalkakakkiya, kirkirarrar al'amari ce. 

Amma babu laifi a shari'an ce mutun ya rokawa kan sa da iyalan sa tsari/kariya daga sharrin shaidan don Allah yace: " Ku roke ni zan amsa muku" Suratul gafir aya 60, ba tare da ware wata addu'a ba ya jingita ga shari'a yace tana maganin kaza da kaza, bayan ba shari'ar ce tazo da haka ba.

Don neman addu'o'in da sunnah tazo da su a nemi littafin (Hisnul Muslim) 

Wallahu A'alam

*Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)