*YADDA ZAKI HADA KUNUN AYA MAI DADIN GASKE*
_DAGA_ 👇
*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞
(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A ✍️
_Kunun aya kala kala ne akwai kunu akwai muna kunu to yau insha Allah zan koya muku yadda uwar gida zatayi kunun ayan da mai gida zai sha yayi santi_
_YANDA ZAKI YI KUNUN AYA ME DADIN GASKE_
Kayan Hadi
*Aya*
*Kwakwa*
*Dabino*
*Sugar*
*Madara*
*Flavor*
Yadda Za Ki Hada Kunun
Ki gyara ayarki ki cire duwatsu da dattin ciki, sannan ki jika a ruwa ta yini ko ta kwana amma idan zata kwana ki tabbata kin canza ruwan gudun kada ta yi tsami, sannan ki cire kwallon cikin dabino ki jika dabinon ki yayyanka kwakwar ki kanana, idan kin zo markada wa sai ki zuba wankar kyar ayar ki a blender, ki zuba kwakwa da dabino a kai kiyi blending ko ki kai inji a markado miki ita, bayan kin markada sai ki tace da kyalle akalla sau biyu, sannan ki zuba sukari da flavor da kankara, idan anzo sha kuma sai a zuba madara ta ruwa ko ta gari.
Shi kunun aya baya son zafi da zaran yayi zafi to zata yi yauki, sai a bar ta a kankara ko a saka ta a frizer..
_Atura zuwa ga sauran group din sbd yan uwa musulmai_
Sigh by✍️
*SIDDIQAHTUL KHAIR Y FARU*