_*👩🍳A A KICHEN FOOD/SANKS👩🍳*_
*DAY-I*
_Shinkafa da miyar albasa,sai haɗin salad da /meat-pie/da/Shayin na'a na'a/da dabino._
*🍚DAHUWAR SHINKAFA🍚*
_*Kayan hadi*_
_Shinkafa🍚_
_Cocomber🥒_
_Albasa🧅_
_Gishiri🧂_
_Mai🍾_
_*YADDA AKE YI*_
_Da fari zaki fara wanke shinkafar ki da ɗan gishiri kaɗan ki tacce ta ki ajiye a gefe sai ki ɗauko tukunyar da zaki dafa ta ki ɗora akan wuta idan ta ɗauki zafi ki zuba mai kaɗan ba da yawa ba sai ki ɗan jefa albasa kaɗan aciki ya ɗan soyu zaki ga albasar tayi ja kar ki bari ta ƙone ƙamshin albasar da man muke buƙata sai ki ɗauko wannan shinkafar da kika tace ki zuba ta a ciki kina juya ta by 5minti sai ki tsayar da ruwan dafa shinkafar taki a kai._
_Bayan kin tsaida ruwan shinkafar ya tafasa ta ɗauko dahuwa sai ki kuma tace ta ki tsane ki kuma mai da ita kan wuta ki saka ruwa dai dai wanda zai ƙarasa dafa ta,bayan ta dahu sai ki kashe wutar ki kwasheta a filas a ido ma zaki ga yanda zatayi washar washar sai ki ɗauko Cocomber ki ki wanke shi tas ki samu wuƙa ki yanka shi siri shiri yankan fadi ki bi shinkafar dakika kwashe a filas ki luluɓe saman da shi ki rufe wannan ƙamshin cocomber shi zai daki shinkafar ya gauraye ta gaba ɗaya😋_
_*👩🍳🫑A A KICHEN FOOD/SANKS🫑👩🍳*_
_*07065014495*_