YAUSHE NE LOKACIN BUƊA BAƘI?



*TAMBAYA*❓

Yaushe ne lokacin buda baki (shan ruwa)?
                     
*AMSA:*👇

Lokacin buda baki ya na tabbata ne da zarar rana ta fadi. 

Dalili kuwa shine, hadisin da aka karbo daga Sahk ibn sa'ad, ya tabbata acikin Sahīhul Bukhārī daga Sahl Ibn Sa’ad yace: haqiqa Manzon Allah yace: 
 
Mutane ba zasu gushe tare da alheri ba matuqar suna gaggauta buda baki.
 
Amma abin mamaki ayanzu sai kaga wadansu mutane suna jinkirta buda baki har sai sunyi sallar magriba. 

Haqiqa yin haka ba qaramin kuskure bane, domin ya sabawa koyarwar Manzon Allah. Wadan suma sai kaji su na cewa sai taurari sun bayyana, sannan suyi buda baki. Irin wadannan mutane a tunanin su yin haka shine daidai, alhali kuwa ya sabawa Sunna, kamar yadda akayi bayani a hadisin daya gabata.

Haka hadisin da aka karbo daga Abdullahi Ibn Abī Auf yace: "ya kasance tare da Manzon Allah (SAW) a lokacin tafiya suna azumi, sai rana ta fadi, sai Manzon Allah (SAW) yace da wani daga cikin sahabbansa ya sauka ya shirya musu kayan buda baki sai, sahabin yace: "Ya Manzon Allah da sauran rana, akayi haka har sau uku, Manzon Allah na cewa dashi ya shirya musu abin buda baki. Daga karshe bayan sun kammala sai Annabi yace: “Idan kuka ga dare ya gabato daga nan (wato rana ta fadi), haqiqa mai azumi ya bude bakinsa (ana nufin koya sha ruwa ko bai sha ba)

Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.

ALLAH NE MAFI SANI

Zaku iya samu wannan group na telegram ta wannan hanyar👇

https://t.me/joinchat/Bdi85VSaiLc5NGQ0
Post a Comment (0)