HUKUNCIN KISS TA HANYAR WAYA



*HUKUNCIN KISS TA HANYAR WAYA!!* 

*TAMBAYA*❓

Assalam alaikum.Malam SHIN ya halatta mutun
yayiwa budurwarsa KISS yayin da suke waya, idan har an bashi ita kafin suyi aure?

*AMSA*👇


Wannan yana daga cikin ire iren abubuwan da fitsararrun samari da 'yan matan zamani
suka Qirkiro. Kuma yana daga cikin abubuwan da suke cire musu kunya, kuma yake afkar dasu acikin zina.
Misali_ saurayi da budurwar da suka saba yiwa Junansu Kiss ta waya, da zarar sun hadu FACE TO FACE, babu abinda zasuyi tunani illa
su aiwatar da Kiss din azahiri.
Irin wadannan al'adun turawa ne, bai dace
da dabi'unmu da addininmu ba..
Mu a addininmu ba'ayin kowanne irin Kiss sai bayan an daura muku aure da juna.
Annabi (saww) yana cewa: ''Kunya tana
daga Imani. Duk wanda bashi da kunya, to bashi da Imani.."
kuma yace "DUK WANDA YAYI KAMA DA WASU MUTANE, TO TABBAS YANA CIKINSU".
Don haka duk wanda yake so ya haifi
'ya'ya masu albarka, to wajibi ne ya nuna
dabi'u masu kyau irin na Musulunci tun
alokacin neman auren mahaifiyarsu.

WALLAHU A'ALAM.

 Allah ya shirye mu baki daya, Yasa masu yi su daina. Ameen

https://t.me/joinchat/Bdi85VSaiLc5NGQ0
Post a Comment (0)