ABUBUWA GOMA 10 DA SUKE SA MUTUWAR ZUCIYA
Babban Tabi'i Ibrahim bin Adhama (R.H), wata rana yazo wucewa ta kasuwar Basra, sai mutane suka taru akansa suka kewayeshi, sai suka ce masa ya Baban Ishaq, Lallai Allah yana cewa a cikin littafinsa "KU ROKE NI ZAN AMSA MUKU" amma munayi ba'a amsa mana, sai ya basu amsa da cewa: zuciyoyinku ne suka mace daga abubuwa guda goma (10)
✿ Kun san Allah amma baku ba shi hakkinsa.
✿ Kuna karanta Al-'Kur'ani amma baku aiki dashi.
✿ Kuna riya cewa kuna son Manzon Allah (S.A.W) amma kuna barin sunnar sa.
✿ Kuna cewa lallai shaidan makiyin kune amma bakwa saba masa.
✿ Kuna cewa lallai ku kuna shaukin son shiga Al-jannah amma bakwa aikin shigarta
✿ Kuna cewa lallai ku kuna tsoron wuta amma bakwa aikin guje mata.
✿ Kuna cewa lallai mutuwa gaskiya ce amma bakwa mata tanadi.
✿ Kuna shagaltuwa da sa ido akan laifukan mutane amma kuna mantawa da naku
✿ Kuna cin Ni'imomin Allah (S.W.A) amma bakwa gode masa.
✿ Kuna binne matattunku amma bakwa daukar izina dasu.
Sai Baban Ishaq yace; Ta yaya za'a amsa muku.
# Zaurenfisabilillah
Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah