*MAKARANTAR AZUMI 021* //
```📌ALAMOMIN DA AKE GANE DAREN LAILATUL QADRI```
*ALAMOMIN WANNAN DARE* : ana gane alamomin sa tunda Rana ne.
*Na farko* : Rana ba ta haske a dukkanin daren da zai biyo baya na wunin Lailatul Kadri misali, idan daren da za’ayi Yau zai kasance Lailatul Kadri ne to Rana bata zafi, za tayi sanyi ko kuma tayi lullumi ya zama ma kamar bata fito ba.
*Na biyu* : Idan daren yayi za’aji tsit Karnuka basa haushi, ba hayaniya, Gari yayi lumana saboda Mala’iku ne ke saukowa su cika duniya a lokacin suna cewa aminci Allah ya tabbata gare ku, zasuyi tayin haka ne har ɓullowar Al-fijir.
Wannan dare a cikin sa ne Allah Yake tsara duk wasu alamura na Shi; don haka yana da kyau dan uwa ya dage wajen yin Addu’o’i kamar yadda muka faɗa a cikin wannan dare Allah yake tsara komai, wane zai mutu wane zaiyi arziqi wane zai talauce, dan’uwa kada ka kuskura ayi babu kai, koda kana da kasala a sauran kwanaki na watan to kada kayi kasala a wannan goma ta karshe ɗinnan, mafi ƙaranci koda Sallar Asham ne ta ranar da aka ajiye Azumi na ashirin 20 to daren da za’a shiga shine daren ashirin da ɗaya 21 to ka samu ko Sallar Asham ce ayi ta a gama dakai (ba lallai sai Sallar cikin dare ba) ita ma ɗin idan har kana da ikon tashi ka samu ka tashi ɗin, kayi ta Addu’o’i kamar yadda hadisi yazo daga Nana Aishah (RA) tace: nace: Ya Manzon Allah ﷺ! Mai kake gani idan na san wani dare ne Daren Lailatul Ƙadri, wace Addu’a zan fada? Sai yace da ita: “Kice: *Allahumma Innaka Afuwwun Tuhibbul Afwa, Fa’fu Anni* ”.
Hakim ya riwato shi kuma ya Inganta shi.
Saboda haka, a goman ƙarshe zage-damtse ake ƙara yi dan uwa wajen yin Ibada da raya dare, da Salloli na Nafilah da Karatun Al-Qur’ani kamar yadda hadisi yazo daga Nana Aishah (RA) tace: Manzon Allah ﷺ ya kasance idan Goma ta shiga – ma’ana goman karshe na Ramadana – sai ya ƙara zage damtse wajen Ibada, ya dinga raya Dare, sannan kuma ya tashi Iyalan Sa.
Bukhaariy da Muslim ne suka riwaito shi.
Kuma ana sa ran ganin wannan dare ne a mara wato wutiri; kamar 21 da 23 da 25 da 27, ma’ana idan akace Yau ankai Azumi na ashirin ne (20) to da zaran Magriba ta faɗi daren da za’a shiga shine daren 21, haka ma idan ankai azumi na ashirin da biyu (22) to daren da za’a shiga shine na Ashirin da Uku (23) domin dare ne ke fara zuwa a Musulunci, kuma kamar yadda Nana Asiha ta ruwaito mana tace ne Annabi yace mu nemi daren a wutiri, Allah muke roƙo yasa mudace da wannan dare, Amin.
✍ *ANNASIHA TV*