*MAKARANTAR AZUMI 023* //
📌 ```I’ITIKAFI```
*SHAR’ANCIN SHI* :
1- Yin I’itikafi Sunnah ne a Watan Ramadana da wani watan da bashi ba a wasu kwanaki na shekara, asali gameda haka shine faɗar Allah: “alhali kuna I’itikafi a Masallatayya”, tare da samuwar Hadisai ingantattu da suka zo gameda I’itikafi daga Manzon Allah (SAW), kuma an samu ayyukan Sahabbai sun zo gameda hakan, duk waɗannan bayanai sunzo a cikin littafin Al-Musannaf na Abubakar Ibn Abu Shaibah da Musannaf na Abdurrazaq.
Hakika ya tabbata lallai Manzon Allah (SAW) yayi I’itikafi a goman ƙarshe na watan Shawwal kamar yadda Nana Aisha ta ruwato, Bukhaariy da Muslim suka fitar dashi a littattafan su, haka kuma yazo daga Sahabi Umar ɗan Khaɗɗab yace ma Annabi (SAW): na kasance nayi alwashi tun a Jahiliyya zanyi I’itikafi a wani dare cikin Masallaci mai alfarma? Sai Annabi yace: “ka cika wannan alwashi naka”, [sai ya samu wani dare yayi I’itikafin nashi], shima wannan hadisi Bukhaariy da Muslim ne suka riwaito shi.
2- Sai dai yafi ƙarfi idan akayi shi a watan Ramadana, saboda hadisin da yazo daga Abu Hurairah: Manzon Allah (SAW) ya kasance yana I’itikafi a kowane Ramadana tsawon kwanaki goma, amma a yayin da Ya kasance a shekarar da aka karɓi ran Manzon Allah a cikin ta sai yayi I’itikafin tsawon kwanaki Ashirin (20), shima Bukhaariy da Ibnu Khuzaimah suka riwaito shi.
3- Yafi falala idan akayi shi a goman ƙarshe na Ramadana, saboda Annabi (SAW) Ya kasance Yana I’itikafi ne a goman ƙarshe na Ramadana har Allah ya karɓi rayuwar Shi, shima Bukhaariy da Muslim ne suka riwaito shi.
✍ *ANNASIHA TV*