*MAKARANTAR AZUMI 020* //
📌 *DAREN LAILATUL QADRI (DAREN DARAJA*)
Wannan Dare yana da falala mai girman gaske, domin a cikin shi ne aka saukar da littafi mafi daraja wato Al-Kur’ani, littafin da yake jagoranci ga wanda yayi riƙo dashi riƙo na gaskiya, zuwa ga hanyoyi na ɗaukaka da daraja, kuma yake ɗaukaka ma’abocin shi zuwa ƙololuwar daraja madauwamiya, kuma al’ummar Musulmi waɗanda suke bin Sunnonin Manzon su (SAW) sau-da-ƙafa, basa ɗaukar wasu bukukuwa suna yi saboda wannan dare mai albarka, sai dai abunda suke yi shine ƙoƙarin yin rige-rige wajen Kiyamul-Laili a cikin sa, suna masu Imani da kuma neman lada a wajen Allah.
*FALALAR WANNAN DARE* : ya isa daraja ga wannan dare kasancewar sa yafi Watanni dubu alkhairi. Allah yace: ( *(mun saukar da Al-Qur’ani a DAREN DARAJA (1) kasan Lailatul Kadari? (2) Lailatul Qadri YAFI WATANNI DUBU alheri (3). Mala’iku suna sauka a cikin sa har da Mala’ika Jibrilu da izinin ubangijin su, abisa yadda ya tsara (4) aminci ne (shi daren) har zuwa ɓullowar alfijir* *(5)* )). _Suratul Qadri: 1-5_
Zamu fahimta wani abu cikin Surar da ta gabata, na daga ciki;
- Samun Ibadar Lailatul Kadri tafi Watanni Dubu yafi kayi ibadar Watanni Dubu, ma’ana kayi Wata Dubu kana bauta ma Allah to idan wani ya dace da lailatul kadari ya fika, don haka yana da kyau mutum ya dage ƙwarai da gaske wajen yin Ibada a wanann Dare, kuma ana so ne mutum ya dinga raye dareran goman karshen don anan ake sa ran ganin ta, kuma ya tashi Iyalan sa suma, sannan ya nisanci Iyalan sa, kamar yadda Nana Aisha ta ruwaito mana haka daga Annabi (SAW) cewa haka yake yi.
✍ *ANNASIHA TV*