FITAR MANIYYIN DA BAI SA AYI WANKAN JANABA



FITAR MANIYYIN DA BAI SA AYI WANKAN JANABA 

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

*TAMBAYA*❓

Salamun alaykum ya shykh antashi lafiya. Tambayata shine 
Idan maniyyi ya fita ajikin mutun ba tare da ya sadu da mace ba shin wanka zai yine ko kuma tsarki kawai.

 *AMSA*👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Idan har maniyyi ya fito daga jikin mace ko namiji, fita ta al'ada, sha'awa ko ta dalilin saduwa da iyali, babu wani banbancin hukunci tsakanin su, mutum zai wanka ne ba tsarki ba. Rashin tuna yadda ya fita ko lokacin da ya fita ba shi bane abin lura ba a nan. 

Amma idan maniyyi ya fita ne saboda tsananin wahala ko wata azaba da ta auka wa mutum, nan ne zai yi tsarki kawai, ya isar masa ba sai yayi wankan janaba ba. 

Wallahu ta'aala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)