JARUMAI GUDA GOMA WAƊANDA KO NI NA SAMU DAMA ZAN IYA YI MUSU DUKAN TSIYA.

JARUMAI GUDA GOMA WAƊANDA KO NI NA SAMU DAMA ZAN IYA YI MUSU DUKAN TSIYA.

Jaruman fina-finan Indiya sau da dama suna iya yin abubuwan ban mamaki a fim, amma a zahiri ba lallai su iya ba, hakan ya sa na kawo muku jerangiyar sunayen jarumai goma waɗanda ko ni na samu dama zan iya yi musu dukan tsiya.

 1. Ranbir Kapoor



Ko da yake jarumin ya ƙware wajen iya soyayya da raye-raye, idan aka zo fannin jarumta shi ba komai bane. Ba shi da siffa ta jarumai kuma ba shi da ƙarfin zuciya, wannan ma ina ganin zuwa ɗaya in na yi masa ya wadatar da shi. 

 2. Mahesh Babu



Duk irin jarumta da izzar da wannan jarumi yake nunawa a fina-finan sa kawai aikin darakta ne. Amma yadda yake kyarara ɗin nan kamar kwanɗagi, da za mu haɗu a lungu, dukan tsiya zai sha. 

 3. Abhishek Bachchan



Akan ce kyan ɗa ya gaji ubansa, amma shi dai wannan ko kaɗan bai gado na shi ba. Da ka gan shi ma ka ga me zubin ragwaye. Wannan ma mazga ɗaya zan mai ya faɗi ƙasa. 

 4. Varun Dhawan



Wannan kam gwanin rawa ne da iya barkwanci, amma duk da haka zai iya taɓuka abin arziƙi, sai dai zai yi saurin gajiya, ni kuma hakan ne zai ba ni damar suburbuɗe shi. 

 5. Vijay



Me Adda, wannan gayen ya daɗe yana rainawa mutane hankali a fina-finansa saboda ya mori masu bada umurni, amma da za mu haɗu a fili shi ma da ya ji ata. 

 6. Vishal



Dogo da hankali dace ne. Wannan kam in da yake yin abubuwa zalam-zalam ɗin nan kamar raƙumi, shima mazga ɗaya zan yi masa in sai ta masa hanya. 

 7. Jackie Shrooff



Ga shi dai uban daba ne, kuma yana ƙaryar ƙarfi, izza da rashin tausayi. Sai dai a zahiri tsufa ne ya yi gardama, domin zuwa ɗaya zan mai a wuce wurin. Sai dai kuma in ya turo min ɗansa, anan ne fa za a yi ta. 

 8. Sonu Sood



Manta da irin abubuwan da kuke gani ana nunawa na murɗewar jiki da tarin ƙwanjin wannan jarumi a cikin fim, girma ba ya ci. Kana samun lagonsa ko kai ma kana iya yi masa dukan tsiya. 

 9. Nawazuddin Siddiqui



Ayya! Wannan har ma ya bani tausayi, shi wannan bar shi dai ace da bindiga a hannunsa, amma in dai faɗa hannu da hannu ne. To ko idona a rufe yake sai na ba shi kashi. 

10. Pawan Kalyan



Ɗan rainin hankali lamba ɗaya kenan. Kawai don ya maida mutane kayan wanki, kawai sai ka ga yana ta jibgarsu kamar ba gobe. Duk barazana ce kawai, kana tare shi a lungu za ka ga ya fara ba ka haƙuri. Tare shi dai a lungun ne kuma yake da matsala.


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
  08185819176 
Haimanraees@gmail.com

2 Comments

Post a Comment