JARUMAN INDIYA GUDA GOMA WAƊANDA ZA SU IYA YI MAKA SHEGEN DUKA.
Da yawan masu kallon fina-finan Indiya sun yarda cewa irin ƙarfin da ake nuna jarumai suna da shi a fim, a zahiri ba haka abun yake ba. Wannan dalili ne ma ya sa wasu suke ganin cewa akwai jaruman da ko su ma za su iya yi musu duka, amma sai ka ga an ba su ƙarfi a fim suna ta jibgar jama'a. To ko da yake akwai ƙamshin gaskiya a cikin maganar, ga wasu jarumai guda goma waɗanda ina ba ku shawarar kada ku yarda ku ce za ku tare su da faɗa ko da wasa.
1. Vidyut Jammwal
Wannan jarumi tun yana ɗan shekara uku a duniya ya fara samun horo na musamman, bugu da ƙari kuma, mahaifinsa tsohon soja don haka ya gaji jarumta. A ƙalla jarumin ya ziyarci ƙasashe 25 tare da samun horo daga maban-bantan masana a harkar faɗa. Ba a ɗaɗe ba ma wata jarida ta bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da ba za ka so ka kara da su ba a duniya baki ɗaya. Don haka duk mai son jikinsa ya yi tsami ta yadda ko magana ba zai iya yi ba, ina ba shi shawarar ya tunkari wannan jarumi da faɗa zai samu biyan buƙata.
2. Salman Khan
Baya ga kasancewarsa mutum me saurin fushi, Salman Khan ƙaƙarfan gaske ne, sannan yana atisaye sosai. Ga shi kuma yana da saurin hannu. Wannan dalili ya sa ba kowa ke iya kawo masa wargi ba, domin kuwa yanzu sai jikin mutum ya yi tsami, masu tsaron lafiyarsa ma kaffa-kaffa suke yi da shi.
3. John Abraham
Ko da ganin kura aka ce wai ta ci kare. John Abraham yana daga cikin jaruman da suka fi kowa yawan motsa jiki, sannan dama can yana da sura da zubi irin na masu ƙarfi, kuma yana da ƙarfin a zahiri. Bugu da ƙari, in ka yi masa ba daidai ba, ba zai ji nauyin Suburbuɗarka ba.
4. Sanjay Dutt
Uban daba me lasisi kenan, shi kam wanna dama da ka gan shi ka ga ɗan ta'adda, don haka ba sai na yi maka dogon zance ba, da zarar kun haɗu kawai ka yi maza ka fece.
5. Prabhas
Jarumin Ɗan tawaye ba wai kawai soyayya da kafce ya iya ba. Jarumin ya kasance mutum ne mai ƙarfin gaske, kuma tun bayan fitowar fim ɗin Baahubali na ɗaya da na biyu ya share wa kowa tantama akan jarumtarsa, don haka in ma kana tunanin za ka iya da shi, to ka yi marmaza ka sauya akala.
6. Akshay Kumar
Wataƙila ka yi tunanin ai wannan sarkin barkwanci ne da iya bada dariya, abin da kawai ya iya kenan. Ayya! Gara ma ka canja tunani, domin kuwa Mr. Khiladi ƙwararrren ɗan kareti ne da sauran salon faɗa makamantansu, hasali ma, tun kafin ya shigo Bollywood ya ƙware a fannin faɗa da ɗaukar kasada, don haka in ka nemi yin karo da shi, to kuwa tabbas za a yi babu kai.
7. Ram Charan
Hatsabibi kenan! Dama can shi wannan jarumi ya gado hatsabibanci a wajen mahaifinsa, da ya girma kuma sai ya ƙara ɓullo da nasa salon. Bugu da ƙari, jarumin yana atisaye sosai kuma yayi fina-finan jarumta iri daban daban da suka tabbatar da wanzuwar jarumtarsa. Don haka shi ma ba kanwar lasa bace.
8. Allu Arjun
Idan ka na so ka ci dukan tsiya cikin salo da ƙwarewa, to yi maza ka tunkari wannan jarumi da faɗa. Ina mai tabbatar maka da cewa za ka samu cikar burinka har ma da ƙari da gyara baki ɗaya.
9. Hrithik Roshan
Bincike ya nuna cewa, da ace za a yi faɗa na fili kuma hannu da hannu, to a kaf daɗin jaruman Indiya mutum biyu ne kawai za su iya cin galaba akan jarumi hrithik Roshan, sune Vidyut da John Abraham. Wannan magana kuwa ba cika baki bace, kasancewar jarumin murɗaɗɗen Sadauki ne da mafi yawancin fina-finansa ma na faɗa ne. Don haka in kana so ka yi jinya ta tsawon lokaci, maza sai ka je ka tare shi da faɗa.
10. Ajay Devgn
Singham! Zaki kenan, jarumi Ajay daɗe yana fina-finai a Bollywood, duba da irin yadda ya ke iya ɗaukar fina-finan faɗa, muna da tabbacin cewa a fili ma zai iya aiwatar da hakan. Bugu da ƙari kuma ya san kan tsiya, don haka duk wanda ke ganin kamar da cinta, sai jaraba ya gani.
©️✍🏻
Jamilu Abdulrahaman
(Mr. Writer)
08185819176
Haimanraees@gmail.com