KABBARBARI A RANAKUN IDI



*MAKARANTAR AZUMI 030/* /


📌 ```KABBARBARI A RANAKUN IDI``` 

An Sunnanta yawan Zikiri da Kabbarbari da faÉ—in La’ilaha Illallah a kwanakin Idi, kuma Musulmi zasu bayyanar da (Kabbarbarin) ne a cikin Gidajen su da Masallatan su da Kasuwannin su da kuma kan Hanya.

Lokutan Kabbarbari a Idin Sallah Ƙarama yana farawa ne tun lokacin da Mutane suka fito domin tafiya wurin Sallah har zuwa lokacin da Liman ya tashi domin yin Huɗuba.

Haƙiƙa ya tabbata daga Magabata (Sahabbai) yanda ake yin wadannan Kabbarbari a Idi; na daga cikin su:

 *Na Farko* : “Allahu Akbarul-lahu Akbar, La’ilaha Illal Lah, Allahu Akbar, Walillahil Hamd”.

 *Na Biyu* : “Allahu Akbarul-lahu Akbar, Allahu Akbar, Walillahil Hamd, Allahu Akbar Wa Ajall, Allahu Akbar Ala Ma Hadana”.

 *Na Uku* : “Allahu Akbarul-lahu Akbar, Allahu Akbar Kabeera”. 


 *LADUBBAN RANAR IDI* 

Ranar Idi ta kasance tana da wasu Ladubba waÉ—anda ya kamata ace Musulmi ya Ladabtu dasu; na daga ciki:

1.    Taya Murna da wannan Idin ta hanyar Mutum yace ma Dan uwan sa Musulmi “Taqabbalallahu Minna Wa Minkum”.

2.    Bayyanar da Farin Ciki da Murna, tare da sanya sababbin Tufafi, da kuma bayar da kyaututtuka, da wasu abubuwa wadanda suke kama da hakan.

3.    Yalwata ma Kai da kuma Iyali da wadanda suke makusantan ka ta hanyar data dace batare da Al-Mubazzaranci ba.

4.    Tausasa tare da tausaya ma wadanda suke Talakawa ne da Miskinai ta hanyar ciyar dasu, tare da kuma kokarin sanya musu farin ciki suma a zukatan su.

5.    Yafiya da kuma kawar dakai ga duk wanda ya maka ba daidai ba, da kuma sulhunta wadan kaga suna rikici. 

 ✍ *ANNASIHA TV*
Post a Comment (0)