LADUBBAN SALLAR IDI



*MAKARANTAR AZUMI 029* //

📌 ```LADUBBAN SALLAR IDI``` 


Lallai Sallar Idi tana da wasu Ladubba, wanda ya kamata Musulmi ya adontu dasu, na daga ciki: 

1-   Wanka, da kuma Ado, da sanya Turare, tare da sanya Tufafi mafiya kyau.

2-   Cin abu kamun a fita wajen Sallah amma a Idin BuÉ—a-baki (Ƙaramar Sallah), da kuma kame Baki daga barin Ci a Idin Layya (Babbar Sallah) har sai an dawo bayan Sallah.

3-   Tafiya wajen Sallah a Ƙafa ba akan abun Hawa ba sai idan har akwai buÆ™atar abun hawa É—in.

4-   Yin Kabbarbari a yayin tafiya wajen Sallar Idi, wannan Sunnah ce ta Annabi da Sahabbai, sai dai a wannan zamanin Mutane har kunya suke ji aga suna Kabbarbari akan hanya, wanda kuma yin hakan bayyanar da wata Ibada ce daga cikin Ibadun Musulunci.

5-   Canza Haya a yayin dawowa daga wajen Sallah. 

 *SIFFAR YANDA AKEYIN SALLAR IDI:* 

Sallar Idi tana da Raka’o’i ne guda biyu (2) ba’a yi musu Kiran Sallah ko Iqama, kuma ba’a sallatar wata Sallah ta Nafila kafinta ko bayanta, kuma ba'a yin HuÉ—uba kamun Sallar sai bayan an kammala Sallah ake yin HuÉ—uba.

Sannan Limami zaiyi Kabbara guda Bakwai (7) ne a Raka’ar Farko; tare da Kabbarar Harama, Kabbara Biyar kuma a Raka’a ta Biyu; amma banda Kabbarar tasowa daga Raka’a ta Farko.

Kuma ana bayyanar da Karatu ne, sai dai an Sunnanta mishi ya karanta a bayan Fatiha dayan fuskoki guda biyu (2):

1-    Suratul A’ala a Raka’a ta farko, da Suratul Gashiyah a Raka’a ta biyu.

2-    Suratul Qaaf a Raka’a ta farko, da Suratul Qamar a Raka’a ta biyu.

Sannan sai Limami yayi Huɗuba guda ɗaya bayan an sallame Sallah, yana mai tsaye akan Ƙasa, kuma yana mai fara Huɗubar tashi da Godiya da Yabo ga Allah; wato Khuɗbatul Hajah wacce itace Huɗubar da Annabi yake yi har ma yake koyar da Sahabban Sa.

✍ *ANNASIHA TV*
Post a Comment (0)