💧💖💧
LAFIYAR ZUCIYARKA
Ka rika bincikar zuciyarka, ka na yi mata service lokaci bayan lokaci don tabbatar da lafiyarta, domin miyagun cutukan zuciya su kan iya shiga ba tare da ka sani ba, irin su kafurci, shakka, munafurci, shirka, son rai, riya, kyamatar gaskiya, k'iyayya ga muminai, K'eta, hasada, girman kai, son duniya, jiji da kai da debe tsammani daga rahamar Allah da sauransu... Saboda haka Ka kasance a farke da yanayi da halin da zuciyarka take ciki, domin da gyaruwanta ne dukkan jiki yake samun tsira...