MAGABATA NA GARI.....
Sheikh Muhammad bn amin shanqidi
Shehin musulunci, gwani a tafsiri, d'aya cikin ababen mamakin da duniyar musulunci ta gani wajan k'arfin kwakwalwa da saurin halarto da abu.
An haifesa shekara ta (1325 h)
Ya kammala haddar qur'ani cikin shekarunsa na haihuwa 10.
Kusan ya haddace kaso mafi rinjaye cikin hadithai ingantattu.
An tambaye shi game da sirrin qarfin haddar sa yace
" mu a garin mu (shanqid) komai haddacewa muke yi."
Yace da kansa" babu wata ayah cikin qur'ani face nayi bincike akanta maqurar yadda zan iya.
Babu wata ayah da wani daga cikin magabata yayi bayani akanta face ina sane da me yace.
Ya fassara fadin allah (أهبطوا مصرا).
cikin awah HUDU 4 ba tare da maimaita wata kalma ba, kuma bai fita daga ma'anar ayar ba.
Wata rana yayi darasi sai aka kai mar cassette din yaji shi da kanshi yace=
"Wai ni nake way'annan bayanin???
Shi da kanshi yayi mamakin yadda yake halarto da abubuwa cikin lokacin qanqani tare da bayanai na ilimi.
Ina tuna wata magana ta Dr Muhammad sani umar r/lemo(hafizahullah) yace
Idan kana so kaga makwafin sheikhul islam bn taimiyya wajan iya jero ayoyi masu alaqa da juna da yin bayani gamsashshe akan su to ka saurari sheikh aminul shanqidi.
Ya fassara qur'ani daga farko har zuwa qarshe sau biyu a rayuwar sa, ya rasu yana kan na ukun dai dai fadin allah
(أُولَٰئِكَ حِزْبُ اللَّهِ أَلَا إِنَّ حِزْبَ اللَّهِ هُمُ الْمُفْلِحُون)
Ya kasance abun koyi wajan gudun duniya da tsantaseni, idan ka ganshi zaka dauka mutumin QAUYE ne ba wanda ke zaune cikin madinar manzon allah ba saboda irin kayan da yake jikin sa.
Yace da kansa" Nazo daga garin mu na shanqid da wata TASKA wacce tana wahalar samuwa, da dai ace naso samun duniya to nasan hanyoyin samun ta, amma bazan fifita duniya akan lahira ba.
Littafinsa na tafsiri, na daga cikin littafan da malamai ke yawan yiwa dalibai wasiyya da karatu cikin sa, domin tarin fa'idodin dake cikin sa,
Yana wahala kaji ya ambaci wani da wani abu face ALKAIRI, anyi shaidar ba a tab'a yin GIBAR wani mutum a majalisin sa.
Ya rasu safiyar ranar alhamis 17 ga watan zulhijja (1393 h) bayan ya gama aikin hajj,an mar sallah a masallaci mai alfarma na makka, kuma a kamar salatul Ga'ib a masallacin manzon allah a madina.
Allah ya jiqan sa da rahma ya bamu ikon koyi da rayuwar sa.
M.A IBRAHIM
ABU MUBEENAH
@Kmsunnah
https://t.me/kmsunnah/1940