SAƁANIN FAHIMTA



SAƁANIN FAHIMTA

ruвutαwα
Nasiru Kainuwa
02022021

An yi abu ko an faɗi magana yadda ka fahimta daban da yadda aka so ka fahimta. Ko kuma ka aikata abu ko ka faɗi magana manufarka daban yadda aka fahimce ka daban. Irin wannan rashin fahimtar ke haifar da saɓani, saɓani kuma shi ne ke haifar mana da matsalolin da muke fama da su, har ta kai ga an yi rikici. Ya kamata idan ba a fahimci mutum ba a nemi ƙarin bayani da ga wajensa, ta haka ne za a kaucewa fahimtar al'amura a baibai.

Ya na da kyau mu riƙa yi wa juna uzuri, kada mu na hukunci da ka, idan mutum ya yi ba daidai ba ƙira shi, wane ka yi abu kaza, wataƙila bai san ya yi ba a rashin sani ya yi, wataƙila ya na sane ya aikata bai zaci ranka zai ɓaci ba. Wani abu kuma da shi ma ya ke haifar mana da matsaloli ko kuma na ce saɓani shi ne, dan kana shugaba ko dan ka isa da mutum ka masa hukunci ba tare da ka ba shi damar kare kansa ba, dan wance ko wane ɗanka ne ko ƙaninka ko kuma yaron ka ne sai aka ce yayi abu kaza, maimakon ka ji bahasi sai ka kama shi da faɗa ka hana shi magana saboda ka na gada da cewa ka isa da mutum ko dan ka na tunanin wanda ya kawo ma sukan ba zai yi ƙarya ba. Duk babba ko shugaba mai irin wannan ɗabi'ar ya na tafka kuskure komai girmansa ko tarin iliminsa. Allah isa ni ma kun fahimci bayanin da na yi, wanda bai fahimta ba ya nemi na masa ƙarin bayani.
Post a Comment (0)