MARIGAYI JANAR ATTAHIRU ABU UKU NE BABBAN LAIFINSA A GURIN MACIYA AMANAR TSARON NIGERIA



MARIGAYI JANAR ATTAHIRU ABU UKU NE BABBAN LAIFINSA A GURIN MACIYA AMANAR TSARON NIGERIA

1- Janar Attahiru yana da gaskiya da amana da tsoron Allah, yana kula da ibada sosai a matsayinsa na Musulmi, yana son ya ga bayan Boko Haram, kuma bai da tsoro, jarumi ne na gaske, masu son ayi gaskiya da amana a wannan zamanin sunfi kowa shan wahala da fuskantar barazana na kisa

2- Ya tona asirin maciya amanar tsaron Nigeria wadanda sukaci kudin makamai a wannan Gwamnatin, abinda ake ta kokarin a rufa, shi kuma yaki bada hadin kai, hatta mai bawa shugaban kasa shawara akan tsaro ya jaddada abinda janar Attahiru ya fada na cinye kudin makamai da akayi a wannan Gwamnatin

Amma idan zaku tuna, hankalin maciya amanar tsaron ya tashi, sai da suka sa shi kanshi mai bawa shugaban kasa shawara akan tsaro ya fito ya janye daga goyon bayan Janar Attahiru akan batun bacewar kudin makamai, kuna tsammanin zasu bar Janar Attahiru da yake son ya kwance musu zani a kasuwa ya wanye lafiya?

3- Batun mutuwar Shekau, daga jiya zuwa yau duk intelligence da spy da suke fitowa daga jejin Sambisa abinda suke fada mana kenan Shekau ya mutu amma babu tabbas, na sha fadin cewa Shekau 'dan ta'adda ne da ba'a son mutuwarsa, saboda maciya amanar tsaron Nigeria na cin riba da rayuwarsa, imba haka ba da tuntuni Shekau ya zama tarihi

Idan ya tabbata Shekau ya mutu dole maciya amanar tsaron Nigeria su zargi Janar Ibrahim Attahiru, sannan zasu iya zama sanadin rasa rayuwarsa a hatsarin jirgin da ya faru da shi yau ya mutu

Wallahi ba'a son Boko Haram ya kare saboda an mayar da ta'addancin babbar haja na neman kudi, nayi rantsuwa da girman Allah ta'addancin Boko Haram ko 'yan sanda bai fi karfin su magance ba, balle uwa uba sojoji, amma ya gagari duk jami'an tsaron Nigeria saboda babu gaskiya

Dole a fito ayi magana ta gaskiya koda za'a mutu, bai kamata acigaba da tafiya haka ba a Nigeria, ta yanda sai dai a kyale maciya amanar tsaron kasa suyi yadda suka ga dama

Kowa zai mutu, duk wanda yake raye yanzu babu wanda zai kara shekara 200 nan gaba a duniya face muna karkashin kasa, mai shirya makirci don a kashe wani kar ya fasa, idan ya isa ya tabbata a duniyar kar ya mutu

Duk ranar kwanan duniya babu na lahira, haka duk ranar kwanan lahira babu na duniya sai an mutu don dole

Allah Ka karbi shahadar Janar Attahiru
Allah Ka la'anci maciya amanar tsaron Nigeria Ka tona musu asiri, Ka watsa al'amarin su Yaa Allah
Post a Comment (0)