MIJI NA MANEMIN MATA NE, YA ZAN YI?



*MIJI NA MANEMIN MATA NE, YA ZAN YI?*

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. ALLAH Ya kara ma malan lafiya tare da imani. Ga tambaya na kuma dan Allah malan ka bani shawara dan samun mafita. Malan Mijina ne ya kasance mutum ne wanda Allah ya azurta shi da abun hannu daidai gwargwado, amma wallahi kudin baya tafiya ko ina sai ta hanyar mata, Miji na manemin mata ne na fitar hankali, ni da nake matar sa bai damu da ni ba kamar yanda ya damu da Matan waje. Ka huta lafiya


 *AMSA*👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah.

Baiwar Allah ki ji tsoron Allah, ki zauna zaman lafiya da mijin ki, ki riƙe auren ki, da fari wannan ita ce shawara ta gare ki.

Kin ce mijin ki manemin mata ne na fitar hankali, yaya aka yi kika san haka?

Bayan haka a ƙasar Hausa, idan aka ce da mutum manemin mata ne, ma'ana fa, shi mazinaci ne. Ita kuma zina tana da wahalar tabbatarwa, shi yasa musulunci yace duk wanda ya jefi wani ko wata da aikata zina, toh ya kawo shedu guda huɗu, hatta zamanin Annabi, har ya bar duniya, ba'a samu ba, sai dai iƙirari.

WaÉ—anne matakai kika É—auka wajen ganin kin yi nasarar hani shi neman matan banza?

Wace irin addu'a kika yi mashi tsakanin ki da Allah, a matsayin gudammawa ta soyayya gare shi da al'ummar musulmi, Allah ya raba shi da wannan mummunan hali?

Wace hanya kika bi domin gano dalilin da ya jefa shi neman mata na fitar hankali da rashin kulawa da ke a matsayin ki na matar shi?

Kuma idan har haka mijin ki yake kamar yadda kika ambata, toh a yanzu, zaÉ“i ya rage gare ki, kina iya samun iyayen ki su shigo cikin al'amarin ku don jan kunne da sulhu a tsakanin ku. 

Ko kuma idan zaman ne kika gaji da shi, toh menene kike ci gaba da yi da shi tun lokacin da kika san shi manemin mata ne, kuma kin yi iya ƙoƙarin ki, magabata sun yi magana amma abu bai yi ba, har zuwa yanzu?

Ko shakka babu bai halatta mu zauna da fasiqi ba, shi yasa tun da farin al'amari aka hana mu auren fasiqi sai dai a rashin sani. Duk lokacin da fasiƙancin miji ya baiyana, akwai matakan da shari'a ta shimfiɗa mana, sai mu bi su sau da ƙafa don kawo gyara da sulhu tare da kuɓutar da shi daga halaka.

Ma'aurata mu ji tsoron Allah, mu daina mummunan zargin juna, mu daina fasiƙantar da junan mu a kan wasu shubuhohi na waya ko text ko chat da dai sauran su, wannan ita ce shawara ta gamammiya ga Ma'aurata.

Shawara ta gare ki ta gaba, ita ce ki natsu, ki duba tsakanin ki da Allah, idan kina kiyaye dokokin Shi, yaya kuma tsakanin ki da shi mijin ki, idan kina kyautata mashi, iyayen ki da ƴan uwa, maƙwabta, kina kiyaye salloli da sauran abin da shari'a ta wajabta maki gwargwadon hali? Don kar ya zamo Allah na azabtar dake ne a sanadiyyar rashin ɗa'ar ki ga Allah da Manzon Shi ne.

Wallahu ta'aala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: 👇_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)