MU KYAUTATA AMFANI DA WAYOYIN MU !!!



MU KYAUTATA AMFANI DA WAYOYIN MU !!!
.
Waya ta zama wani jigo a rayuwar mutane na wannan zamanin. Ina ma ace yadda mutane suke kusantar wayoyin su haka suke kusantar ALLAH da ambatonsa.
.
Haqiqa Waya tana daga cikin abubuwa da suka fi rashin nauyi da sauqin d'auka anan Duniya...
.
Domin idan ka dubi rayuwar al'ummah zaka ga cikin 'yan sakonni ko mintuna mutane basa iya jurewa ba tare da sun duba wayoyin su ba.
.
Sai dai kash !!! Ita wannan na'ura tana iya kasancewa mafi nauyin abubuwa da wahalar d'auka a lahira...
.
Domin yahudawa sun qirqire ta ne domin ta zama ma'abociyar shagaltar da mutane ga qauracewa abunda ke gaban su.
.
Sai dai baza su ta6a samun nasara ga ma'abota hankali da nitsuwa da hangen nesa ba, domin masu tunani suna shagala da wayoyin su ne ta hanyar qira zuwa ga addinin ALLAH da sunnar Annabin Rahma.
.
Waya ta mallaki hanyoyi guda 2 sune: Alkhayri da Sharri.
.
Magabata sun kasance :
.
"كانوا يذكرون الله قياما وقعودا وعلى جنوبهم"
.
"Suna ambaton ALLAH a tsaye da zaune da kan kui6insu "
.
Mu kuma yanzu muna jujjuya wayoyinmu a tsaye da zaune da kan kui6inmu !!!
.
Yi qoqari kayi amfani da wayarka ta hanyar da ya dace domin duk abunda ka aikata da ita:
.
"كل أولآئك كان عنه مسئولا"
.
Ya ALLAH kamai damu zuwa gareka mai dawa mai kyau, ka sanya mu masu aikata alkhayri da wayoyin mu (Ameen)

✍️ Sheikh Aliyu Sa'id Gamawa
Post a Comment (0)