LAMARIN DUNIYA
Bismillah da sunan Allah Rahimi
Shi ya yi akuya kuma shi ya yi raƙumi
Ba ya gajiya balle ya yi gumi
Ba ya damuwa balle ya yi tagumi
Shi ya yi Bauchi kuma sannan ya yi Gumi
Ba ya ƙaunar duk wani azzalumi
Tsira da amincin Allah mai yawa
Gun sahibi abin son kowa
Manzon Allah abin son kowa
Har alihi sahabu gaba ɗaya.
Da ba ka ayau kuma ka yo wanzuwa
Yau ga ka a baina kana yin rayuwa
In ka ji ƙishi a gefe ga ruwa
Babu yunwa kuma ba ka da damuwa
Ka saki jiki kana yin rayuwa
Kan lahira fa ba ka komuwa
Kullum buri yana yin hauhawa
Ka ɗau harka kana cin kasuwa
Ko ka noƙe ba ruwanka da kowa
In ka so ka zamo abin son kowa.
Watarana a ganka kana yin dariya
Kana shagali jin daɗin duniya
Ka sayi gida ga tarin dukiya
Ka hau mota kana bin hanya
Kana harkarka ba wata tankiya
Mulki ya sa kana yin fariya
Ka ɗau ƙarfe ana ta hatsaniya
Kai ne caca kai ne shan giya
Kai ne bin 'yan matan duniya
Kai dai kawai kana ta fagabniya.
Ko da kullum kana annashuwa
Ko kuma kullum kana a damuwa
Ina talaka da ba shi da dukiya?
Ko tajiri mai tarin dukiya
Aure kike yi koko budurwa
Lebura kake ko ɗan kasuwa
Ko da rini kake ko fawa
Ko da tuwo kike siyarwa
Ko ka shina ko kai mantuwa
Watarana tabbas za ka macewa.
Ya 'yan uwa mu zam gyaran hali
Don rayuwarmu tana da dalili
Mu sani dukkanmu muna kan hanya
Kuma za mu tafi babu ragin ɗaya
Fatan kowa ya zam dacewa
Da yin kalima a loton mutuwa
Sai dai kowa ba ya son mutuwa
Kuma za ta zo babu makawa
Alheri munka yo ko sharri
Za mu yi jawabi a kabari.
Ya Allah sarki na roƙe ka
Ka yi gafara ka yafe laifuka
Ka yi rangwame ka yafe mu duka
Ka ƙara mana son addininka
Da Imani da tsantseni duka
Da bin koyarwar manzonka
Ka samu cikin ceton manzonka
Don ni'ima cikin falalarka
Ka sa mu cika muna bin addininka
Ran lahira mu tashi a addininka.
©️✍🏻
Jamilu Abdulrahaman
(Mr. Writer)
08185819176
Haimanraees@gmail.com