Ramadaniyyat 1442H [13]
Dr. Muhd Sani Umar (hafizahullah)
____________________________
1. Duk da cewa Banu Isra’il sun samu annabawa da yawa da aka aiko zuwa gare su, amma duk cikinsu babu wanda ya kai Annabi Musa (A.S) tarin mabiya wadanda suka shahara, amma duk da haka ga irin yadda halinsu ya kasance tare da shi.
2. Amma da aka taho zuwa kan Annabi (ﷺ) sai aka samu a cikin shekaru ashirin da uku (23) kacal, ya samar da gagarumin canji a cikin al’umarsa, ya kafa daularsa. Duk kabilun Larabawa suka zo suka yi mubaya’a a gare shi, kamar yadda Allah ya tabbatar da haka a cikin [Suratu Nasr: 2]
3. Babu shakka wannan yana nuna girman wannan Manzo (ﷺ) da darajar da yake da ita da kuma irin tasirin da ya bari a cikin al’umarsa, musamman sahabbansa.
4. Wannan shi zai nuna maka ashe sukar sahabban Annabi (ﷺ) da cewa su mutane ne marasa gaskiya, kokari ne na kawar da wannan nasara da Allah (SWT) ya ce ya ba wa Ma’aiki (ﷺ); kamar yadda Allah ya ce: (Idan nasarar Allah ta zo da kuma bude (Makka). Ka kuma ga mutane suna shiga cikin addinin Allah kungiya-kungiya. To ka yi tasbihi da yabon Ubangijinka, ka kuma nemi gafararsa. Lalle Shi Ya kasance Mai karbar tuba ne.) [Nasr: 1-3]
5. Annabi (ﷺ) bai bar duniya ba sai da wannan nasara ta tabbata. To kokarin rushe sahabbai shi ne kokarin rushe wannan nasarar da Allah ya tabbatar masa, watau nuna cewa, Annabi (ﷺ) ya tafi ya bar mafi yawan sahabbansa suna makaryata, mayaudara, maha'inta. Kai har ma manya-manyan cikinsu ba su tsira ba; wadanda su ne abokan shawararsa kuma aminansa, su kansu aka jefe su da miyagun maganganu da manyan laifuka wadanda da za a jefi wani karamin mutum cikin ‘yan baya-baya daga cikin wannnan al'umma da irinsu, to da babu shakka zai ce an ci zarafinsu.
6. Don haka masu sukan wadannan bayin Allah wadanda suka fi kowa kusanci da shi, nuna wa duniya cewa; addinin Musulunci ba addini ne da zai iya gyara dan’adam ba, domin ga shi shi kansa wanda aka ba wa addinin ya zo ya koma ba tare da ya ci wata nasara ba. Ka ga babu shakka wannan qaryata Alkur’ani ne, sannan kuma karyata ingantaccen kundin tarihi ne da yake nuna akasin haka.
7. Annabi (ﷺ) bai bar duniya ba sai da Musulunci ya kafu. Sai da ya samu lamincewa daga Allah (SWT) cewa, nasararsa ta tabbata kuma fatahi ya samu.
8. Dole ne Musulmi su bude idanuwansu tar su san cewa, muguwar manufa ce a samu wadanda za su rika fitowa karara suna zagin sahabban Annabi (ﷺ), suna cin mutuncinsu. Ya zama wajibi a kan Musulmi idan ya ga irin haka ya fahimci ina aka dosa? Watau an doshi rushe addinin ne daga tushensa da kuma kokarin rushe martaba da nasarar da shi kansa Annabi (ﷺ) ya samu wadda Allah (SWT) ya ce ya ba shi.
https://t.me/miftahul_ilmi