💊 SHAN MAGANI DOMIN TSAYAR DA HAILA
*Tambaya: Mene ne hukuncin mace ta sha magani domin tsayar da jinin haila don tayi azumi?*
Amsa: ~ Sheikh Muhammad bin Saleh Al-Uthaimin (RahimahulLah) "Abinda nake gani a wannan batun shine cewa; mace kada tayi haka, sai dai ta tsaya akan abinda Allah Madaukakin Sarki ya hukunta ya kuma ƙaddara akan 'ya'yan Annabi Adam (mata), saboda wannan jinin haila da yake zuwa musu akowane wata Allah Madaukakin Sarki Yana da wata hikima wurin samar dashi, wanda wannan hikimar ta dace da yanayin mace, idan har ta tsayar da wannan dabi'a to wani abu zai iya faruwa wanda zai zama cutarwa ga jikin mace, kuma Annabi salati da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: "Babu cuta, babu cutarwa."
Wannan Idan ma bamuyi la’akari da cutarwar da wadannan kwayoyin suke haifarwa ga mahaifa ba kenan, kamar yadda likitoci suka ambata. Dan haka abinda nake gani game da wannan mas'alar shine mata kada suyi amfani da wadannan kwayoyin. Godiya ta tabbata ga Allah akan ƙaddararsa da hikimarsa. Idan hailarta yazo mata ta ajiya sallah da azumi, idan ya ɗauke ta sai ta fara sallah da azuminta, idan ramadhan ta ƙare ta rama abinda ake binta".
#Zaurenfisabilillah