SHEKARA 40 Da suka wuce kowa yana kwadayin ya Tara 'ya'ya. Amma yanzuu mutane tsoron Tara 'ya'ya sukejii
..........................................
SHEKARA 40 Da suka wuce 'ya'ya ke yiwa iyaye biyayya. Yanzu iyaye ke yiwa 'ya'ya biyayya.
........................................
SHEKARA 40 Da suka wuce Aure nada sauki sakin mace keda wuya. Yanzu aurene da wuya sakin macene da sauqi.
........................................
SHEKARA 40 Da suka wuce duk munsan 'yan unguwarmu. Yanzu dan unguwarku kakewa kallon Bako.
.........................................
SHEKARA 40 Da suka wuce har musun fifikon shekaru mukeyi. Yanzu kowa so yake a rage masa yawan shekaru.
........................................
SHEKARA 40 Da suka wuce har gasar fifikon Qiba muke yi. Yanzu kowa gudun qiba yake saboda a burge.
........................................
SHEKARA 40 Da suka wuce Attajirai ke qoqarin nuna suma talakawanee. Yanzu talakawa ke qoqarin nuna suma Attajirai ne.
..........................................
SHEKARA 40 Da suka wuce Mutum daya ke nema kuma ya dauki nayin gidan gaba daya. Yanzu duk gidan ke aiki Dan a dauki nauyi yaro daya.
........................................
DAGA 1980 ZUWA YAU FA SUNE SHEKARA 40.
WANNAN SAUYIN QARARA YAKE KUMA MU MUKA CHANJA DUNIYA BA ITA TA CHANJAMU BA
Allah yasa muga mai kyau. Aameen Yaa Rabbul Izza