UWA TA GARI


UWA TA GARI:

Rubutawa: Sheikh Aliyu Said Gamawa

Mu sani 'yan uwa duk duniya ba mai son mutum kamar mahaifin sa; amma tabbas sai ka ninka son da uba yake yiwa wa dan sa sau biyu kafin ya kai son da maifiya take yiwa dan ta. Madallah da soyayya irin ta mahaifiya.

Mahaifiya itace farkon mafi kusanci ga kowa; in ka lura sosai kusacin yana farawa ne daga daukar ciki, Haifuwa zuwa goyo, reno, shayarwa, addu'a, da kula da lafiyar jiki da kwakwalwar dan ta da bashi tarbiyya.

Uwa tana son danta a boye da bayyane, tana son mai son sa, tana nuna damuwar ta kan rayuwar sa da yawan tunanin sa da kokarin bashi kariya a duk in da zata iya tun daga farko har zuwa karshen rayuwar ta ko tasa.

Wani abin lura ga rayuwar dan Adam shine duk wanda ya dace da samun uwa tagari zaka iya cewa yayi sa'ar samun rayuwa mai dadi don zata dora shi akan turba mai tsabta. Gaisheki uwa ta gari!!

Madallah da uwa ta kwarai mai yabo da addu'ar fatan alheri ga rayuwar danta don wannan addu'ar alheri yana bin wannan dan a duniya da lahirar sa.

Babban abin tsoro tsakanin uwa da dan ta shine ace "UWA" ta sa bakinta mai daraja tana suka ko aibata danta ko yi masa jafa'i, don yadda sanya yatsa a miya kesa miyar tayi tsami haka bakin uwa ke tasiri ga lalacewa da matsala ga rayuwar danta in ta aibata shi.

Bisa wannan nake kira gareku iyayen mu maza da kuna kula da alakar 'ya 'yan ku da iyayen su mata, ku dafawa matan ku wajen kula da yaran su, don mace na da rauni da rashin saurin ganin laifin danta.

Iyaye maza ku sani fa tun daga aure ake za6owa yara uwa tagari...wato duk mai son dan kwarai ya auri mace tagari. 

Iyaye maza ku sani yalwatawa iyalai da taimako uwa ta zauna cikin wadatar kudi alheri ne ga yaran ka.

Na dade ina da wata tambaya a zuciyata wai da ace mahaifin mutum na da dukiya mai yawa ko da ace mahaifiya ce da dukiya mai yawa... wacce ce cikin dukiyar dansu zai fi wadaqa da birgima cikin bushasha wajen more kudin?

Lallai samun uwa tagari mai tsoron Allah da kula da addini da kankan da kai, da uwa mai ilimin addini da tarbiyya yana da matukar amfani da tasiri ga dan ta. 

Hakika tsatso yana naso shi yasa zaka ga da yawa cikin mutane kowa na samun 6angaren kamanni na halitta da gadon hali ko dabi'a na iyayen sa.

Ina addu'ar Allah ya bada ladan raino da tarbiyya ga iyayen mu. Allah ya jikan iyayen mu ya hadamu dasu a aljannah, amin.
Post a Comment (0)