WAI MAI KALLON FILM LOKACIN DA YANA JI ANA KIRAN SALLAH SAI YACI GABA DA KALLO YA AIKATA SHIRKA?

*WAI MAI KALLON FILM LOKACIN DA YANA JI ANA KIRAN SALLAH SAI YACI GABA DA KALLO YA AIKATA SHIRKA?*


https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum.
Dan Allah malam da gaske ne duk wanda yake kallon film yana ji ana kiran sallah yaki zuwa ya yi ya aikata shirka?


 *AMSA*👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah.


Subhanallahi.


Shi dai film iri biyu ne, akwai mai fa'ida da ilmantarwa mai amfani. A shar'ance kallon irin wannan film da zai yi bayanin sallah, Imani, Shirka, Azumi, Zakka, Aƙida, Sanao'i na zamani, Illolin saɓa ma Allah, Iyaye da Shugabanci, Noma, Yaƙi da kafirci da dai sauran ababen da zai amfanar da mai kalloa addini ko a rayuwa, ko duniya da lahira, irin wannan film ya halasta a kalle shi. Amma ko shi wannan ɗin idan mai kallo ya ji ana kiran sallah toh zarcewa da kallo ya haramta a lokacin, haramcin kallon a irin wannan lokacin yana ƙara girmama idan ma aka tayar da iqama, amma ba'a aikata shirka ba. 


Amma nau'in film na biyu shine film maras fa'ida a rayuwa ta addini ko duniya. Irin film ɗin da ɓarnar da yake koyarwa tafi yawa sama da gyara ko amfanin da ke cikin shi, ma'ana dai baya koyar da wata fa'ida ko kuma fa'idar shi kaɗan ce. Kallon irin wannan film ya zamo haram, kamar wanda zai koyar da Zina, Caca, Sata, Ha'inci, Garkuwa da mutane, Zaluntar bayin Allah da basu ji ba, basu gani ba, Baiyanar da tsiraicin maza ko mata, toh wannan film bai halatta a kalle shi ba. Amma idan har mutum ya kalle shi, ba za'a ce ya aikata shirka ba, sai dai ace ya aikata haramun. Shi ma girman zunubin yana banbanta, misali, wanda ya kalli porno (Blue film) yafi girman zunubi sama da wanda ya kalli adventure da babu zina a cikin shi, ko kuma wanda ya kalli wasan ƙwallon ƙafa. 


Don haka maganar da aka ce, wanda ya ji an kira sallah kuma bai halarci sallar ba ya aikata shirka, ba gaskiya bane. Wannan fatawa kuskure ce kawai, Allah ya kare mu. 
Abin da ya haifar da irin wannan ɗanyen hukunci shine jahilci. 


Ma'ana rashin rarrabe tsakanin zunubai ko aiyukan haram. Kowace shirka zunubi ne kuma haramun ce, amma ba kowane zunubi ko haramun bane shirka. Shi yasa Allah ya tabbatar mana da shirka da abin da bai kai shirka muni da girma. ba, 


(إِنَّ ٱللَّهَ لَا یَغۡفِرُ أَن یُشۡرَكَ بِهِۦ وَیَغۡفِرُ مَا دُونَ ذَ ٰ⁠لِكَ لِمَن یَشَاۤءُۚ وَمَن یُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱفۡتَرَىٰۤ إِثۡمًا عَظِیمًا)
[Surah An-Nisa' 48]


A wannan ayah, kalmar Azhiman, na nufin mafi girman zunubi cikin zunubai. Kuma Allah yace yana yafe zunubin da bai kai na shirka ba, idan mutum ya mutu bai tuba ba, amma ga wanda ya ga dama. Toh idan mai karatu yayi nazari, sai ya tambayi kan shi, ina kallon film ya zamo shirka? 


Har ila yau, na daga cikin abin da ya janyo wannan mummunan fatawa, rashin sanin ma'anar shirka. 


A takaice dai kalmar Shirka tana nufin, baiwa wanin Allah (Annabi, Mala'ika, gunki, ko Waliyyi ne) haƙƙin Allah (kamar Ibada, Addu'a, Yanka, Tawakkali, Neman Agaji, Kariya da Tsari, Tsoro (Khaufu) da Fata (Raja'u) da sauran ababen da ake nufatar Allah da su). Ma'ana dai Shirka ita ce karkatar da irin abin da yake na Allah ne, ko kuma babu mai iya yin shi sai Allah, ga wani bawa daga cikin bayin Shi, wannan shine haƙiƙanin Shirka, misali roƙon Waliyyi (matacce ko mai rayayye) Haihuwa, Arziƙi ko Tsari daga wani sharri ko abin tsoro, ko yanka da zubar da jini ga wani aljani ko rauhani. Roƙon Shehi, yayin ziyarar makabarta irin abin da Allah kaɗai zai iya yin shi duk shirka ne, haka ma raya cewa ba Allah ya halicci wani Shehi ba, cewa Shehi ya san muridin shi duk inda yake kuma zai shigar da shi aljanna, duk wannan shine gayar shirka, iyazhan billahi, ba kallon film ba, duk da cewa kamar yadda ya gabata, ana iya samun zunubi a sanadiyyar kallon wasu fina-finai. 

Wallahu ta'aala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)