WANDA YA SHA AZUMI SABODA RASHIN LAFIYA, BA ZAI CIYAR BA !!!



WANDA YA SHA AZUMI SABODA RASHIN LAFIYA, BA ZAI CIYAR BA !!!


Tambaya

Assalamu Alaikum Malam A bani shawara:
 Na kamu da wata cuta ta zubar da yawu wanda bana iya kai azumi yau shekara uku kenan, nasha azumi 23 da farko, shekara ta zagayo ban samu sauki ba na kuma shan 20 kuma ina tsoron kada wata shekaran ta riskeni shine na auno masara mudan nabi 43 akan akwai makwabtanmu yaran marayu ne ,shin idan na basu na biya azumi na ko ko? Nagode


Amsa

Wa alaikumus salam, In har akwai tabbacin ciwon ba zai warke ba ka rama azumin, kana iya ciyarwa.
Amma in har akwai tunanin za ka warke to ba za ka ciyar ba, saboda wajibi akan mara lafiyan da ya sha azumi saboda lalura ya rama a wasu kwanakin na daban kamar yadda Allah yake cewa: "Kuma wanda ya kasance mara lafiya bai azumci Ramdhana ba, to ya rama abin da ya sha a kwanaki na daban" Suratu Al-bakarah aya ta:(185).

Aya ta (184) a cikin surar ta nuna wanda ya sha azumi saboda rashin lafiya ko tsufa kuma babu tunanin ya samu damar ramawa nan gaba zai iya ciyarwa.

A bisa abin da ya gabata In har likita ya tabbatar za ka samu damar ramawa nan gaba to azumin yana nan akanka, ciyarwa ba za ta wadatar maka ba.

Sannan in har ciyarwa ce ta halatta akanka ai ba mudun-nabi ake bayarwa ba !!!

Allah ne mafi sani 

06/12/2017.

*Amsawa:* Dr. Jamilu Zarewa.
*Gabatarwa:* Abu- Unaisa.

👉🏾 Darussunnah Foundation, 07035888158.
Post a Comment (0)