*ZAN IYA YIN RIGAKAFIN CORONA?*
https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA
*TAMBAYA*❓
Assalamu Alaikum sunana Abdulrahman daga Algeria, Ina miqa gaisuwa zuwa ga malaman zauren nan, Dan Allah ina so a mana fatwa kan Vaccine din Coronavirus. Saboda doktoci da yawa suna nuna cewa akwai abubuwa da yawa cikinsa da zai iya ma mutane illa.
.
*AMSA*👇
Wa'alaykumussalam
.
Shi dai riga kafi a bune da addini musulunci ya tabbatar da shi, babu laifi ayi...
Amma idan bincike na masana ilimin likitanci kwararru wadan da ake kyautatawa zaton masu tsoron Allah ne ya nuna cewa a cikin sinadarin da ake riga kafi da shi akwai illa toh sai shari'a ta hana ayi amfani da wannan sinadarin sai dai a nemi wani, domin Allah yana cewa : "kada ku jefa da hannayen ("kan ku cikin halaka") Bakara 195.
A wani wurin yana cewa : "kada ku kashe kawunan ku..." Nisa'i 29.
.
Abisa wannan ne zamuce idan haka ya tabbataba toh bai halatta ayi amfani da wannan sinadarin ba sai dai a nemi wani wanda babu cutar wa.
.
Amma idan mujarradin maganganu ne na mutane kawai babu wani bincike daya tabbatar da gaskiya al'amarin toh babu laifi mutun yayi har sai ya samu bayani sahihi akan illar dake ciki.
Wallahu A'alam
Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177