ZAN IYA YIN KARI WAJAN BIYAN BA SHI?


*ZAN IYA YIN KARI WAJAN BIYAN BA SHI*

Tambaya
Assalamu alaykumu. Wani ne ya tambaye ni cewa "ya halatta idan mutum ya bada bashin kudi idan an dawo Masa da bashin a hada Masa da kyauta daga Wanda ya bashi bashin saboda Wai ya taimake Shi da ya ba shi bashin kudin a lokacin da yake buqata. Shin ya halatta ya karba Karin kudin a matsayin kyauta Kari akan bashin da ya bayar.? Jazakallahu khairan Dr.

Amsa
Wa alaíkum assalam,
In har ba mai bashin ne ya nema ba ya halatta, saboda Annabi (SAW) ya taba cin bashin rakumi da ya zo biya sai ya bayar da Wanda ya fi shi, sai yake cewa: "Zababbunku su ne masu kyautatawa wajan biyan bashi" Kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi a hadisi Mai lamba ta (1316).

In har Mai bashin ne ya nema to ya zama ribar da Allah ya tsinewa.

Allah ne mafi sani 

Amsawa..
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
28/02/2021

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)