AL'ADA TANA DA TASIRI A ZAMANTAKEWAR AURE !



AL'ADA TANA DA TASIRI A ZAMANTAKEWAR AURE !

*Tambaya*
Assalamu alaikum Malam, idan mutum na da mace fiye da daya, Allah ya ba shi arziki ya kai su saudiyyah, suka yi aikin hajji, to malam idan ya kara.aure idan zai biya mata hajji dole sai ya biya musu su duka? Wai shine adalci? Don yana ganin lokacin da ya biya musu ba ta nan, ba ta da hakki akai, yanzu kuma duk suna nan duk suna da hakki akai.

*Amsa*
Wa alaikum assalam,
A zahiri ba zai sake biya mata ba, saboda ya kai ta HAJJI ne don ta sauke farali, shi kuma Hajji sau daya ya wajaba a rayuwa, ita kuma ta biyun ba ta sauke ba, wanda hakan ya bambanta su.

Al'ada tana da tasiri wajan yanke hukunci, wannan yasa ake so a koma gare ta, in an samu rikici.

Allah ne mafi sani

Amsawa✍🏼

*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

01/06/2021
Post a Comment (0)