DEAR AMARYAR BAYAN SALLAH



DEAR AMARYAR BAYAN SALLAH
  
Assalamu Alaikum 

 Amaryar bayan sallah da uwar amarya, kawaye, ango and all 'yan gayya masu burin a kece raini ranar bikin wane da wance.

It is very, very, absolutely very unfortunate that our beautiful lives have been reduced to nothing but wedding glamour and photos.

Kullum kwanan duniya yanzu a Nigeria biki akeyi kamar ba gobe. Idan ka ga irin kudin da ake kashewa event daya kama daga hall din, decoration, food da kayan sawa sai ka rantse ba the same Nigeria bace da ake fama da yunwa, talauci da kuncin rayuwa ba. Bukatar kawai shine da bikina, ko na 'yata ace zancensa ya zaga bakunan jama'a kowa maganar haduwarsa yake yi. Believe it or not this is a serious setback-why? Because we have better things to do with arzikin da Allah Ya bamu. Ba ina nufin idan kuna da kudi kada ku yi abin burgewa ba, by all means make your day special. Amma abin dubawa yanzu shine darajar biki ta daga 100% akan yadda mu ka sani a shekarun da su ka gabata haka ma mutuwarsa. Shirin da ake yi ba na zaman gidan auren bane, iyakarsa taron jama'a kawai. Sai bayan sati biyu ko kasa da haka ka ga ma'auratan sun fara yawo a social media with one complain or the other about their beloved spouse suna neman shawara saboda sun tarar da auren ba yadda su ka yi zatonsa ba.

Just imagine hall din biki na wuni daya N5M wani without food fa! Kayan amarya atleast a lalace irin iyayenta are not that well to do ta saka from head to toe worth 100k. Za'ayi watanni ana planning special couple entrance saboda shi ma abin yayi ne. Da bikin su wane ba karamin daukar magana suka yi ba, mine will be even better....haka dai rayuwa babu wani focus shi kanshi auren babu wani tanadi da ake masa sama da shagalin biki. Yaya zaman zai kasance after all the merriment??? OHO!

Uwar amarya ta hana kanta da maigida kwanciyar hankali tana son bikin 'yarta ya fi na 'yar gidan kawarta ko 'yar uwarta burgewa. Aci bashi na fitar hankali a kawata biki da gidan amarya. Biki zaiyi kyau haka ma gidan wadanda akayi domin a burgesu zai burgesu din. Shin iyakar gudunmawar da ya kamata ku bawa 'ya'yanku kenan a yayin da su ke shirin fara sabuwar rayuwa?

Kawaye 'yan taya bera bari kuna nan kuna kai dinki na tsantsar fitsara da rashin kunya ana tara kudin kwalliya a fito babu mayafi. It is now all about exposing as much as you can ki burge as many as you can....shi mutumci madara ne, idan ya zube ba'a iya kwashe shi gabadaya. A word is enough for the wise.

At the tail end of all these comes the photos to be posted on social media most especially on instagram. Ke kanki amarya kin sani wani shiri da kike yi da dama ba don angonki bane, so kike kawai idan anyi hoton nan ki fito kiyi kyau. Wani ya biki da wow wani ya biki da mtseww. Da wanda ya isa da wanda bai isa ba kowa ya gani ya tanka shikenan, indai akwai LIKES to duk inda ta fadi sha ne. Kuyi ta karkace kai da baki a rangada kwalliya a dau hoto kawai don duniya ta gani. Duk mun koma ababen tausayi saboda mun manta ainihin abinda ake nufi da rayuwa da guzurin gobe kiyama.

'Yan uwa watan Ramadan mai falala amma ina da yakinin some of us are eager ya wuce saboda bukukuwan da suke gabanmu. Aure is good, aure martaba gareshi amma not the kind of aure da muke yi yanzu where all the albarka has been drained tun a wajen biki.

Please let us all think 10 times or more about our lives. Indai hoto ne kiyi ado da kaya masu tsada kin saka don ki tada hankalin wadanda kika fi believe me the world has seen dubunsu. A wannan zamanin babu abinda zakiyi da ba'ayi ba. Abu daya ne ya rage mana duka as long as muna rayuwa-neman dacewa duniya da lahira. Duniyar a rikice take da abubuwan daukar hankali da nesantamu daga ni'imar Allah da muke hari ranar lahira. But still mu dage mu yaki zukatanmu gwargwadon iyawarmu.

Remember, we are Muslims, and in Islam there are bridges that are not meant to be crossed, not because of gazawa, rashin wayewa ko son dakusar da baiwar da Allah Ya haliccemu da ita. Ko kadan, decency in everything is priceless for one mistake, one son zuciya, one bin yarima a sha kida may cost you more than you bargained for.

#Remain# #blessed#
 @sheikh abdul👳🏽‍♂️

#BarkaDaSallah.
Copied
Post a Comment (0)