*Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambayata 6,483:*
=
Shin idan yaro qarami wanda baya magana yayi atishawa za yimashi hamdala ne ko gaishe dashi za'ayi?
=
=
Amsa
=
_Toh wannan Idan Kaduba Cikin Kashshaful Qina' juzi'insa na biyu shafi na 158. Sukace idan yaron yana iya fayyace abu mekyau da mara kyau wato yayi wayau kenan to inyayi atishawa se akoya masa fadin Alhamdulillah, inyace Alhamdulillahi se ace masa Yarhamukallah. Hakama sukace sabon Musulinta da mutumin kauye suma duk idan sunyi atishawa to se akoya musu fadin Alhamdulillah. Inkuma yaron bame wayau bane toh anan se malaman sukayi sa6ani. Wasu sukace idan yayi atishawa se wakilinshi yace Alhamdulillahi a madadinsa. Wakili anan kamar mama ko baba ko yaya ko wani babba. Amma wasu malamai suna ganin babu batun a wakilceshi tunda baze iyaba to kawai shikenan, kuma wannan shine zancenda muke akansa. Sekuma wasu malamai sukace idan yaro karami irin wannan yayi atishawa toh balallai se ance masa Yarhamukallahuba kowacce irin addu,a ana iya yin masa ko ace yagfirukallah ko ace Burika fiyka. Amma Imamun Nawawi acikin Al-Azkhar dama wasu malamai su suna ganin babu bambanci tsakanin babban da yaro kawai shima ace masa Yarhamukallah, kuma wannan shine abunda muke kai. Wallahu ta'ala A'alam*****_
=
=
Allah Yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
°
Yau
14-06-1441
09-02-2019
=
=
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
Domin samun shafinmu a Telegram
https://t.me/joinchat/IqYRYUcyJstfI3sSYKPKsQ
°
Kuna iya samun tsoffin darussanmu kai tsaye ta cikin wannan shafin
http://www.zaurenkitabuwassunna.blogspot.com
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika