YAR MADIGO???



'YAR MADIGO???
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*MAJALIS - SUNNAH*
.
.
مجلس السنة
📓📔
+2349032091131
+2348142323858
.
.
Yau 07/ 10/ 1440 wanda yayi dai-dai da 30/ 05/ 2019.
=
=
_Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyuakanmu. Hakika Wanda Allah ya shiryar Babu Mai 6atar dashi, Wanda ya 6atar Kuma Babu mai shiryar dashi. Kuma Ina Shaidawa babu abinda bautawa da Gaskiya sai Allah shi kadai, kuma ba shi da abokin tarayya. Kuma Ina Shaidawa Muhammad bawansa ne Kuma manzonsa ne._

_Bayan haka, a gaskiyar lamari ba yanzu na so nayi wannan bayanin ba, tho amma saboda wasu dalilai ne yasa zanyi bayanin a takaice insha Allah._

_Idan akace Madigo ana nufin saduwa ta hanyar gogayya tsakanin macce da mace ta amfani da tsiraicinsu ko cikon halittun matancinsu don jin dadi ko kau da sha’awar junansu._

_Wasu kuma sun bayyana Madigo da cewa, hanya ce ta biya wa kai bukata da mata ke yi a tsakaninsu da mata ‘yan uwansu. Hakika wannan halayya ta fi zina muni ga al’umma. Halayya ce da ko dabbobi ba sa yin ta. Wannan babbar masifa ce da ta shigo wa al’umma, take kuma habaka da ruruwa cikin al’ummar musulmi._

_A yanzu dai bincike ya nuna cewa a kan samu ‘yan mata daga shekaru goma zuwa sama da haka na aukawa cikin wannan harkar. Za a iya jefa madigo a nau’in cututtukan ruhi wanda shaidan ke fesa wa ‘yan Adam gubarsa. Kamar yadda wata ta gabatar da takardar ta a taron ƙara wa juna ilmi kan matsalolin al’umma musamman madigo ɗin. Ta nuna cewa: “Neman jinsi ya faro ne tun daga zamanin Annabi Lut a.s wanda ya zo a tarihi cewa Shaidan ne ya zo a siffar ‘yan Adam ya nuna wa mutanen Annabi Lut a.s yadda za su rika neman junansu. Shiyasa zuwan Musulunci ma ya kawo ma hukuncin masu aikata wannan cewa kisa ne ta hanyar jefo su daga dogon gini”._

_Hakika a shekarun baya baza muce babu wannan abu ba, amma ko da akwai tho ba a jin hirarsa sosai sai yanzu ne yake ƙara habaka. Amma yanzu me ya jawo abin ya taso ya habaka har yana neman samun gindin zama a kasashenmu?_

_Dalilai da suke haddasa yawaitar madigo da farko akwai kaucewa addini da ya umarci iyaye da su aurar da yaransu da wuri yayin da suka kai minzalin balaga. Amma maimakon haka sai a dauka cewan hakan ƙauyanci ne, don haka a bar yara mata su yi karatu mai zurfi. Wanda kuwa a wurin karatun wasu ke haɗuwa da wannan bala’in yanayin da ake barinsu suke cakudawa da wasu masu halin. Shiga cikin taron kawaye inda masu iri halin suke na taimakawa._ 

_Tho a irin haka wasu har gida za su rika biyo ta, uwa ta saki baki ai kawayen ‘yarta ce don haka sai a shigo a shige daki. A irin wannan ne zaka ga ita ma ta zama gwana in ba ayi sa’a ba har kannenta ta ba ta. Auren mace mai irin wannan hali. Misali mutum ya auro amarya bai san tana harkar ba kuma yana ‘yan mata da suka girma. A irin haka matar kan ja ra’ayi wasu daga cikin yaran don sa su cikin wannan harkar musamman ma idan suna taya amaryar kwana in ba girkinta bane sai a zaci shakuwa ce mai karfi a tsakaninsu amma abin da take koyawa yarinyar kenan. Daga nan yarinyar ita ma ta ƙware har ta koya wa wasu ita ma. Haka kuma makarantar ke taimaka wajen samun irin waɗanda suka samu irin wannan mummunar ɗabi'a, da zarar ta samu masu irin halin shikenan sai abin ya cigaba da yaɗuwa. Musamman in an samu sakacin hukumomin makarantu. Idan hukumomin makarantun kwana za su kafa kwararan matakai na tsaro a dakunan kwanan dalibai. Sannan ya zama wani maudu’i guda mai zaman kansa da lokaci zuwa lokaci za su rika tunatar da dalibai a kansa da illolinsa. Sannan in suka kama ma suyi su zartar da hukunci tho da abin ya yi sauki kwarai._

_Itama ƙafofin sadarwa wannan ma hanya ce mai saukin yaduwar wannan masifar. Misali idan aka dubi ‘dandalin Facebook’ akwai kawai sai ka ga guruf-guruf sun fi ɗari na ‘Lesbian’ ‘yan madigo, wadanda kawai wannan abu ake a ciki. Kuma abin takaici cikin kaso 100 ƙashi 90 Hausawa ne ‘ya’yan Musulmai suna maganganunsu na batsa, har da tura hotunan da bidiyo na wannan bala’in domin kara dulmiyar da Musulmi kuma suna ajiye lamba, in da mai bukatarsu. Jama'a ku duba abinda yake faruwa a irin wannan lokacin, kaga mace ta fito da duwawunta tana rawa ana daukarta a video, kuma a yada videon a kafafen sada zumunta, Kunga duk irin wannan kofa ce ta Yan Madigo, kuma dama yawancin masu yin hakan yan madigon din ce._

_Samuwar fina-finan ba sun karfafa abin ta hanyar jefo mana mugayen fina-finai na batsa ta hanyar kasa-kasai ko tauraron ‘yan adam. Tun suna turawa kyauta har yau abin ya zama da kudi ake saya ta Intanet saboda raja’ar da mutane suka yi kansa. Irin wannan fina-finan zallar abin da suke nunawa shi ne salo-salo na yadda jinsi daya za su biya bukatarsu da juna cikin sauki._

_Hikimar Yahudawa ta turo wannan balai ɗaya ne da na Shaidan, shine su dulmiyar da mutane ga sabon Ubangiji. Wadannan suna cikin abubuwan da suka taimaka ƙwarai wajen yaduwar wannan cuta ta Madigo. Duk da cewa Shaidan la’anannen Allah shi ya kawo mana tallar wannan masifa tho amma fa a zamanin nan yan uwansa Yahudawa sun taimaka sossai._

_Matsalolin da madigo ke haifar wa masu yinta 1. Yana haifar da mugun ciwon mara duk yadda masu madigo suka kai ga dabara da kwarewa ba za su taba kancewa kaman suna tare da namiji ba. Hakan kuma yana nufin wannan ruwan yana taruwa ne a mararsu a hankali kuma yana daskarewa har ya taru ya zame masu ciwo mai tsanani mara jin magani._

_2. Yana haifar da cuta tun daga farji har izuwa mahaifa wadda wannan cutar kuma tana iya hana haihuwa kwata-kwata, baya ga gusar masu da sha’awa na maza._ 

_3. Yana haifar da ciwon nan na hanji wannan cutar na hanji ita ke haifar da gudawa ba tsayawa sai dai ga mutum na tsiyayewa._ 

_4. Yana sanya ciwon ruhi, ciwon ruhi ba ciwo ne da ake sha masa magani ko allura ba. Ciwo ne da yake kekashe zuciya ya sanya imani ya fita daga cikinta ya zamo dan Adam ya fita daga haddin mutane yana kuma iya aikata abin da dabbobi ma ba za su iya aikatawa ba._

_5. Yana haifar da cutar mantuwa mutum ba zai iya riƙe abu a ƙwaƙwalwarsa ba, misali za ka yi abu yanzu da shi amma zuwa anjima zai manta, sannan kuma yana rage kaifin basira._ 

_6. Yana rage masu sha’awan mazan aurensu._

_7. Yana taimakawa wajen yaduwar cutar sida (Kanjamau)._

_8. Yana kashe masu sha’awa gaba ɗaya._

_9. Yana kashe aure, kamar yadda muke gani a zahiri._

_10. Yana kashe zuciyar masu yin sa._

_Allah Ubangiji ya ƙare mu da sharrin wannan bala’in._
=
=
_Dan uwanku a musulunci_ 
°
*_✍Abdulrasheed Ibn Musa Abms_*
*_(ABU-MANAL*
°
°
.
Allah ta'ala yasa mudace
.
.
https://www.facebook.com/Zauren-Majalis-Sunnah-420869088334488/?referrer=whatsapp
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Post a Comment (0)