FAHIMTAR MARVEL 001
SASHEN FARKO NA FINA-FINAN DUNIYAR MARVEL CINEMATIC UNIVERSE
Fina-Finan Marvel dai a yau sun kai in da suka kai, domin kuwa babu wani saƙo da lungu da labarin su bai shiga ba ko a hotuna ne. Wani abu na musamman kuma mafi burgewa dangane da waɗannan fina-finan shi ne, ko da yake cewa kowane fim yana cin gashin kansa ne, gaba ɗaya labaran fina-finan suna alaƙa da juna ta yadda in kana kallonsu za ka iya fahimtar yadda labarin fim kaza ya ci gaba daga in da ya tsaya a fim kaza.
Sashen farko na fina-finan duniyar Marvel Cinematic Universe ya fara ne daga shekara ta 2008 zuwa 2012 da fina-finai kamar haka:
1. Iron Man
2. The Incredible Hulk
3. Iron Man 2
4. Thor
5. Captain America: The First Avenger
6. The Avengers
YANZU KUMA GA BAYANIN SU DALLA-DALLA
IRON MAN: Hamshaƙin biloniya kuma ƙwararren mai ƙera makaman yaƙi Tony Stark ya samu canjin rayuwa ta har abada bayan da wasu gungun 'yan ta'adda suka sace shi a lokacin da ya je gwajin wani makami a sahara. Bayan sun kama shi ne sai ya ƙera rigar ƙarfe ta yaƙi ya tsere. Daga nan ya yi ta artabu da mugaye in da daga ƙarshe ya haɗu da jami'a Natasha Romanoff wacce aka fi sani da aka Black Widow, da kuma shugabanta na ƙungiyar SHIELD wato Nick Fury.
THE INCREDIBLE HULK: Ƙwararren masanin Kimiyya Bruce Banner ya samu canjin Rayuwa shi ma bayan ya zama bijimin ƙato wanda kullum cikin fushi yake.
IRON MAN 2: Bayan duniya ta gano cewa Tony Stark Shi ne Iron Man. Hakan ya jawo masa maƙiya da yawa tare da abokan adawa. Wannan ya jawo masa ƙasurgumar matsala yayin da wani masani a harkar ƙere-ƙere da be san kowanene ba ya kawo masa farmaki.
THOR: Bayan Yariman birnin Asgard watau Thor ya samu saɓani da mahaifinsa, sai mahaifin nasa ya ƙwace masa dukkan ƙarfin da yake da shi sannan ya turo shi wannan duniya ta mu. A yayin faruwar wannan lamari ne ya koyi darussa masu yawa ciki har da sadaukar da kansa domin wasu, wannan ya sa ya samu soyayyar mahaifinsa a karo na biyu.
CAPTAIN AMERICA:THE FIRST AVENGER: Tsamurarren soja Wato Steve Rogers ya samu canjin rayuwa ta har abada a shekara ta 1940 bayan an yi masa allurar zama sojan ƙarfi na ban mamaki. Ya yi yaƙi sosai kuma ya nuna jarumta kafin daga baya ya faɗa cikin teku da nufin kare al'umma daga bam ɗin da ka iya tashi a jirgin. Bayan kimanin shekaru 70 da faruwar haka, sai aka gano shi a cikin dusar ƙanƙara bai mutu ba.
THE AVENGERS: Dukkan waɗancan jarumai da ka ambata sai suka haɗu waje guda, tare da wani gwanin kibiya mai suna Hawkeye a ƙarƙashin Nick Fury domin kawo ƙarshen harin da ƙanin Thor wato Loki ya kawo wa birnin New York tare da dodanninsa.
Waɗannan fina-finai su ne suka haɗu suka ba da jimillar fina-finan Marvel cinematic universe a sashen farko na fara yin fina-finan su. Kuma in aka lura da kyau za a ga cewa, kai tsaye ana iya cewa labarin nasu ya zo ƙarshe, to amma Marvel suna da hanyoyin tsara labarai da za su iya ba wa kowa mamaki.
A shiri na gaba za mu ji bayanai dangane da sashe na biyu.
# haimanraees
# marvelcinematicuniverse
# marvelstudios
©️✍🏻
Haiman Raees
# haimanraees
Haimanraees@gmail.com
