HUKUNCIN SANYA TURARE GA MACE DON FITA UNGUWA

HUKUNCIN SANYA TURARE GA MACE DON FITA UNGUWA


https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum Malam dafatan kowa lfy
Malam Nice na sanya turare mai kamshi asaman kayana tom danaje gidan kanin mamata sai yake min fada wai hakan bai dace ba infita ina kamshin turare harar jama'ar waje suji inason karin bayani malam Nagode.

*AMSA*👇

Daga Ubaidu Yace :
"Lallai Abu Hurairata, ya hadu dawata mãta wacce ta sanya Turare, Sai Yace Mata: Ina kikeson zuwa ne haka Baiwar Allah? 
Sai mãtar tace: Masallaci zanje.
Sai Yace: Sbd zaki Masallacin ne kika sanya Turare?
Sai mãtar tace eh
Sai Abu Hurairata Yace Lallai nãji Manzon Allah (SAW)Yace"Duk mãtar da ta sanya turare tafita da nufin zuwa Masallaci,
to Allah mai girma da daukaka bazai karbi sallarta ba har saita dawo tayi wanka Irin wankanta na Janaba."
{Ibn mãjah ne ya ruwaito shi acikin KITABUL FITAN babin Fitnatun Nisã'i (4002)
Malaman Muslunci sun inganta hadisin,
Sheik Nasurudden albany yayi ta'aliqi akan haka, yakara dacewa"Idan har(sanya turare sbd) zuwa Masallaci yazama Harãmun toya(ake tunanin) hukuncinsa zai Kasance akan wacce ta sanya shi sbd zuwa Kasuwa,titi da kuma hanyoyi? Babu makawa yin hakan yafi tsananin haramci,

Amma ya halatta taci ado maikyau da turare mai kamshi agidan mijinta da kuma muharranta kamar yanda yazo a Alkur'ani suratul an-nor (31) 

Imam at-taimey yana fada acikin (Az-awãjir 36/2) Lallai fitar mace da zatayi tana mai sanya Turare kuma tana mai kwalliya, yana daga cikin MANYAN LAIFUFFUKA kuma koda mijinta ne yayi Mata izini,kuma duk wadan nan Hadisan wadan da suke nuna haramcin sanya turare ga mace idan zata fita waje) baki dayansu sun shafi gaba dayan lokuta ne Mukhtasar Kitãbu jalbãb Al-mar'atul muslimah (shafi na 44)].

Ya Allah ka shiryar damu da zuriyar mu baki daya.

Allah sa mudace.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: 👇_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)