HARUFFAN HAUSA
Haruffan Hausa sune ƙwayoyin da Hausawa ke amfani da su a yayin ginin kalma ko gaɓa ko jimla, da sauransu.
Haruffan sun rabu gida biyu kamar haka:
BAƘAƘE
Su ma baƙaƙen sun kasu gida uku, ga su kamar haka:
Na Asali ko sanannu
B, C, D, F, G, H, J, K, L, M, N, R, S, T, W, Y, Z
Ƙirƙirarru/gwagware/gajeru/ɗaiɗaiku
Ɓ, Ɗ, Ƙ, 'Y
Masu goyo
FY, GY, GW, KY, KW, ƘY, ƘW, SH, TS
WASULLA
su ma wasullan sun rabu gida biyu kamar haka:
Sanannu/Na asali
A, E, O, U, I
Aure/gwamammu/masu goyo/tagwaye
Ai, Au, Oi, Ui
©️✍🏻
Haiman Raees
Haimanraees@gmail.com