SALLAR YAYEWAR KO WACE DAMUWA



SALLAR YAYEWAR KOH WACE DAMUWA

"Akwai wani mutum daga cikin Sahabban Manzon Allah (saww) daga cikin Al-Ansar (Mutanen Madeenah) ana kiransa da suna "ABU MU'ALLAQ" (ra). Ya kasance shi Attajiri ne yana yin kasuwanci da dukiyarsa da kuma ta mutane.

Yana zuwa garuruwa daban-daban. Ya kasance shi mutum ne mai yawan ibadah kuma mai yawan tsantseni (kyamar haram).

Watarana ya fita domin kasuwancinsa sai ya hadu da wani 'Dan fashi wanda yasha 'damara da makamai kala-kala ajikinsa. Sai 'dan fashin yace masa "Ajiye dukkan abinda ke tare dakai domin ni kasheka zanyi".

Sai yace masa "Mai yasa kake son zubda jinina alhali ga dukiyar nan kaje kayi sha'aninka da ita?".

Sai ɗan fashin yace "Amma dukiya kam zata zama tawa. Amma ni dai babu abinda nake sai zubda jininka".

Sai Abu Mu'allaq (ra) yace "To tunda ka Qi sai ka kasheni, amma ina so ka kyaleni inyi sallah raka'a hudu".

Sai 'Dan fashin yace "Sallaci duk abinda kaso". (Amma dai sai na kasheka).

Sai Sahabin nan (Abu Mu'allaq) yayi alwala ya sallaci raka'a hudu. Yana daga cikin addu'o'in da yayi acikin sujadarsa ta raka'ar karshe yana cewa: 

*Ya Wadood Ya Dhal 'Arshil Majeed, Ya Fa'alun Lima Yureed! As'aluka bi-izzikal ladhee la yuraamu, Wa Mulkikal ladhee la yudhaamu, Wa bi nurikal ladhee mala'a arkaana 'arshika, an takfiyanee sharra hadhal Lissi Ya Mugheethu agithnee, Ya Mugheethu agithnee, Ya Mugheethu agithnee*.

Yayi wannan addu'ar har sau uku. Sai ya hangi wani Mutum akan doki ya taho aguje. A hannunsa akwai wani mashi, ya 'dora akan goshin dokinsa. 

Yayin da 'dan fashin nan ya hangeshi atafe, sai shima ya taho wajensa. Suna haduwa sai ya soke 'dan fashin nan da mashinsa. Nan take ya kasheshi. 

Sannan ya juyo wajen Sahabin nan yace masa "Tashi".

Sai Sahabin yace masa "Mahaifina da Mahaifiyata fansa ne agareka! Shin wanene kai? Gashi Allah ya taimakeni da kai".

Sai mutumin yace masa "Ni Mala'ika ne daga cikin Mala'ikun sama ta-hudu. Yayin da kayi addu'ar nan da farko sai naji Kofofin sammai sunyi wata irin Qara!. 

Sannan kayi addu'ar nan karo na biyu sai naji Mala'ikun sammai sunyi wani irin gunji. 

Sannan kayi addu'ar nan a karo na uku sai naji ance lallai wannan addu'ar wani wanda ke cikin damuwa ne. Don haka sai na roki Allah yayi min izini in jibinci kisan wannan 'dan fashin".

Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace "Kayi sani cewa duk wanda yayi alwala yayi sallah raka'a hudu sannan yayi wannan addu'ar, lallai za'a amsa masa. Ko yana cikin damuwa ne, ko ba acikin damuwa yake ba".

- Amma idan kai zakayi akan wata bukatarka, zaka cire daidai wajen *An takfiyanee sharra hadhal Lissi* ɗin nan. Saika faɗi bukatunka awajen sannan kace "Ya Mugheethu agithnee" sau uku.

#habeebu_m_sabiu
Whtapp 07034953741
Post a Comment (0)