HASSADA

📌HASSADA❗️

'Daya daga cikin magabata yake cewa: "Duk mai gudun duniya (Zuhudu) da kuma Tsoron Allah zai wahala hassada ta same sa"

     Abul Abbas Ahmad bn Abdilhalim (ibn Taymiyyah) R.h ya ce:
"Duk me yin hassada yayi kokari ya dena. Domin tana daga cikin cututtukan zuciya marassa warkewa ga kuma kashe gangar jiki ...."

Dukkan wanda Allah Ta'ala ya mishi wata ni'ima hakan baya nuna ya fika girman matsayi gurin Allah, kaima akwai irin taka ni'imar, nashi bazai rage naka ba, kai yanzu kana jin haushin abinda Allah Ta'ala ya yima bayin sa? sannan hassadarka baza ta sanya Allah Ta'ala ya daina daukaka bayin sa ba, ya kamata Dan Adam ya rika yima kansa nasiha
Muminai zuciyar sa a wanke take daga irin wannan dattin na zuciya.

Mu ji tsoron Allah bayin Allah!

  Allah Ta'ala ya tsare mu hassada da sauran cuttukan zuciya da na gangar jiki gaba d'aya. (Amin) 

#Zaurenfisabilillah 

Telegram:
https://t.me/Fisabilillaaah

Facebook:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/

Post a Comment (0)