ILLAR JINKIRIN TUBA DAGA ZUNUBI.



ILLAR JINKIRIN TUBA DAGA ZUNUBI.
-
💖🥀"Jinkirta tuba daga zunubanka yana da matuƙar illa ga rayuwarka, ita mutuwa dai ba wasu alamun ranar da zata ziyarceka take bayyanar maka ba, sau da yawa za kaji ance wane lafiyarsa ƙalau, amma kuma yau an wayi gari babu shi, wato an karɓi rayuwarsa, da yawan marasa lafiya kuma waɗanda ake yi musu tunanin mutuwar sai kaga Allah ya tashi kafaɗun su"
-
💖🥀"Sau da yawa jinkirin tuba yana haifarwa da bawa jin cewa ba yanzu zai mutu ba, shaiɗan zai ta riya masa cewa koda bai tuba a yanzu ba, to ai yana da sauran lokaci a rayuwarsa, sabida haka sai yaita zugashi yana aikata laifuka ga Allah ba kuma tareda yana neman yafiyar su a gurin Allah ba"
-
💖🥀"Kayi ƙoƙari ka tuba zuwa ga Allah tun kana da lokaci gabanin lokacin ka ya ƙure, tabbas lallai haƙiƙa Allah yana karɓar tuban bawa matuƙar lokacinsa bai zo gargara ba, da zarar lokacin ka yazo gargara, to shikenan Allah ya ruɓe ƙofar karɓar tuba daga gareka"
-
Post a Comment (0)