HUKUNCIN HIRAR BATSA (SEX-CHAT)
https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA
*TAMBAYA*❓
Menene hukuncin Mutanen da sukeyin Sex-Chat, wato hirar batsa ta hanyar rubutun Text ko ta hanyar rubutu a Social-Media musamman ta WhatsApp??
:
*AMSA*👇
:
To itadai hirar da akeyi ta batsa atsakanin Namiji da Mace ta hanyar Ƙiran Waya ko rubutaccen saƙo kamar yadda akafi saninta da sunan Sex-Chatting, ko Shakka babu wannan wata Musibace da Fitina wacce ta addabi Al'ummar wannan Zamani damuke cikinsa, tun daga kan Maza har Mata, masu aure da marasa aure, wasuma daga cikinsu zakasamu cewa Ɗaliban Ilimine, danhaka al'amarin dai sai wanda Aʟʟαн( ﷻ ) Ya tsallakar kawai, itadai wannan hirar batsa takasune gida biyu,
:
(1)-Kodai yakasance Namiji zaiyi irin wannan hirarne da Matarsa itama Mace tayi da Mijinta,
:
(2)-Kokuma ya kasance Mutum zaiyi irin wannan hirarne da Matar da ba tasaba ko Mijin da ba nataba,
:
Idan ya zamana Mutum zaiyi irin wannan hirarne da Matarsa ko Mace tayi da Mijinta, to yakan iya zama Halal amma Saida Sharuɗɗa guda biyu,
(1)-Sharaɗi nafarko yakasance babu wani Mutum akusa dasu ta yadda zai iyajin hirar dasukeyi atsakaninsu idan yazamana suna hirarne ta hanyar Ƙiran Waya, idan kuma ta hanyar rubutune to ya kasance sunkiyaye ta yadda babu wani wanda zai iyaganin hirar dasukayi acikin rubutun, kokuma yaga irin hotunan sassan jikinsu da suka aikawa junansu, balle kuma Mutum yace zaije ya nunawa abokansa ko ita ta nunawa ƙawayenta irin hirar da sukeyi,
(2)-Sharaɗi nabiyu, ya kasance tsakanin Matar da Mijin dukkansu sun aminta da kansu cewa wannan hirar da sukeyi bazata kaisu ga aikata dukkan wani abu ta hanyar wasa da jikinsu wanda hakan zai iya kaisu ga sunfitar da Maniyyinsu ba, wato abinda da akafi sani da suna Masturbation, idan waɗannan Sharuɗɗa guda biyu suka cika to ya halatta ma'aurata suyi atsakaninsu, amma idan hirar zata iyasa wani daga cikinsu kokuma suduka sukai ga sunkasa iya mallakar kansu harsai Mutum yayi abinda zai sashi yafitar da Maniyyinsa to anan suma kansu ma'auratan yazama haramun suyi irin wannan saboda wancan mummunan aikin da hirar zata iya kaisu ga aikatashi, domin a Shari'ance akan iya Haramta abinda yake Halalne idan yakasance zai iya kai Mutum ga aikata Haramun, amma idan yakasance hirace kawai sukeyi atsakaninsu har Sha'awar Mutum takai Ƙololuwa yayi Inzalin-Maniyyi batare da yayi amfani da hannunsa ba ko wani abu dabam to wannan babu laifi ya halatta,
:
Amma idan yakasance ita wannan hirar ta batsa maisuna Sex-Chatting, tana gudanane atsakanin waɗanda ba ma'aurataba wanda kuma dama galibi ita wannan hirar anfi yintane kodai tsakanin Samari da 'Yammata, ko Samari da Matan aure, ko Maza masu aure da 'Yammata, kokuma Mazan aure da wasu Matan auren da ba nasuba, danhaka wannan ko kokwanto babu akancewa yin wannan hirar Haramunne Ƙaulan-Wahidan, danhaka wajibine akan masu wannan aiki suyi gaggawar tuba zuwa ga Aʟʟαн( ﷻ ):
:
шαʟʟαнυ- тα'αʟα α'αʟαмυ
AMSAWA
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: ▽_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*