Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
Ko da ya ke na ce na musulunta, ina sallar karya, ina zikiri, amma a karkashin zuciyata na tabbata ni ba Musulmi ba ne. Kuma da yawa cikin mutanena sun tabbata musuluntana biri-boko ne.
Shiga hannun Mahadi ya dame ni ainun. Amma babban abin da ya fi damuna, shi ne tilas in ya bar mini raina, in zama Bamahade. Tilas im bi shi, tilas in aikata duk abin da ya umurta, im bar abin da ya hana. Ka ji abin da ya fi kona mini zuciya ke nan, watau girmama mutumin da na rigaya na wulakanta har cikin karkashin zuciyata! Im ba tilas ba, mutum ba ya zabar wa kansa wulakanci. Na dai tsai da shawara zam bi Mahadi, ko da ya ke a raina ina nan bisa biyayya ga gwamnatin Masar.
Kashegari da safe na kira Farag Eifendi da Ali Effendi Tobgi, na ce musu na ji shawararsu. Kuma na zaro wasikar Zogal da ya aiko ya ce im bi, na nuna musu. Zogal ya ce in na yarda zam bi, to, mu hadu a Hilla Shiera, ran 23 ga Disamba, don ya ba ni takardar Mahadi ta karbar sulhu. Na ce wa hafsoshin nan na yarda zan nemi sulhu. Sai na kira akawuna na ce ya rubuta wa Zogal na yarda zan zo Hilla Shiera a ranar da ya sa. Da aka rubuta, na tashi manzo ya kai wa Zogal.
Na tara shugabannin rundunata duka, tun daga manjo manjo har ya zuwa kalasaje, na ce musu na karbi shawararsu har na aika neman sulhu. A ran nan da dare na shirya na tashi na nufi Hilla Shiera. Da muka kusa isa garin, na tura yaro guda gaba na ce ya sanad da Zogal gani nan tafe. Muna isa kofar gari sai ga Zogal ya zo tariyata. Ina zuwa inda ya ke na dira daga dokina, ya miko mini hannu da fara’a muka gaisa. Ya miko mini takardar Mahadi. Ko da na buda sai na ga ba maganar sulhu ba ce sosai. A ciki dai an ce Mahadi ya nada Sayed Mohammed Khalid Zogal ya zama gwamnan kasashen Yamma na Sudan. Ni kuma ya karbi sulhuna, ya yafe mini, ya kuma ba dansa Zogal izni ya karbe ni cikin darajar da na ke da ita, haka kuma duk sauran mutanena wadanda ke aikin gwamnati a da.
Da na kare karantawa, Zogal ya ce mini duk wannan alheri bai samu ba, sai domin ya sa hannunsa. Ba don shi ba, da Allah kadai ya san abin da zai faru gare ni. Bayan wannan sai ya janye ni waje guda muka gana, ya tambaye ni iyalinsa. Na gaya masa suna nan a hannuna, amma na daure manzonsa Khalid. Ko kadan wannan bai bata ransa ba, sai ya aika kurum aka zo da su. Amma ya gode mini sabo da rikon kirki da na yi wa iyalinsa.
Ya rubuta takarda ya aika wa Mahadi, ya fada masa irin yadda muka yi. Wajen tsakiyar watan Mayu, sai ga amsa ta dawo daga gun Mahadi, a gaya mini ya karbi sulhuna, amma yana so ya gan ni, don ya san ni fuska da fuska.
Da Sayed Muhammed Zogal Ibn Khalid ya kare karanta mini wasikar Mahadi, sai ya ce in shiga shiri, zai hada ni da wakilinsa ya kai ni gunsa. Da na gama ’yan shirye-shirye, muka tashi a tsakiyar watan Yuni tare da mutum goma daga Fasher zuwa Lubayya. Ka ji farkon rabuwa da ’yancina ke nan!
Tun kafin mu taso, Zogal Ibn Khalid ya fada mini cewa, rashin ruwa ya tashi Mahadi daga Lubayya ya koma Rahad, a can za mu same shi. Ga mu nan har muka iso Rahad. Muka doshi sansanin Halifa Abdullahi, ba mu doshi gun Mahadi ba. Bayan mun gaisa da Abdullahi, ya yi mana 'yan tambayoyi, aka kai mu masauki a sansani. Muna cin abinci, sai ya ce mu shirya mu tafi masallaci, azahar ta yi. Muka yi alwala, ya wuce muka bi shi. Masallacin yana kusa da masaukin Mahadi ne. Muka tarad da jama’a sun taru da yawa. Mahadi shi ne liman, zuwa can ya zo. Muka mike, mu da ke sahun gaba. Ya dubo ni ya ce, “Salamu alaikum.” Na ce masa, “Alaikumussalam
.” Ya miko mini hannu. Ya ce mu zauna, ya yi mana maraba, sa’an nan ya ce mini, “Kana jin dadi ?" Na ce, “Lalle ina jin dadi tun da na zo kusa da kai.” Ya ce, “Allah yai maka albarka. Lokacin da na ji kana ta yake yake da Jama’ata, na yi ta addu’a Allah ya maishe ka Musulmi. Ga shi Allah da Annabinsa sun karbi rokona, ka musulunta. Yanzu za ka bi ni ka yi aikin lada, maimakon bin gwamnati don kudi, kazantar duniya kurum. Ka san wanda duk ya bi ni, ya bi Allah ke nan da addininsa, zai sami farin ciki nan duniya da kuma lahira.”
Wannan shi ne farkon ganina da Muhammed Ahmed Mahadi. Dogo ne, ba fari sosai ba, kakkarfa, mai babban kai, da ido daradara. Yana da kwale uku uku irin na mutanen Sudan, ga hanci har baka, da karamin baki. Kuma mai fara’a ne, in ya yi dariya sai ka ga hakoransa farare fat, sun jeru tantsai, sai wushirya a tsakiyarsu. Suturarsa kullum ba ta wuce yadda na bayyana a baya ba, watau gajeruwar jabba da wando iyaka kwauri, da tagiya makawiyya, ya nada mata dan guntun rawani fari. Su tufafin nan cike su ke da kanshin sandal da na turaren wuta da miski. Kanshin wadannan shi a ke kira ‘Rihatil Mahadi,’ watau kanshin Mahadi, har jahilan mabiyansa su kan ce wai kanshin nan ya fi kanshin aljanna dadi.
Tun kafin mu taso daga Fasher wani ya gargade ni cewa in na zo in ce da Mahadi ya ba ni rantsuwa don in nuna ban gaskiyata gare shi. Sabo da haka bayan ya kare magana sai na ce masa, “Ya shugabana mai tsarki, ina so ka ba ni rantsuwa don ka tabbatad da gaskiyar biyayyata gare ka." Da jin haka sai ya ce in zo in rusuna a gabansa. Da na rusuna ya ce in ce, “Na rantse, zan bi Allah, da Annabinsa, da Mahadi. Ba zan yi shirka ga Allah ba, ba zan saci abin wani ba, ba zan yi zina ba, ba zan cuci kowa ba, ba ko zan ki bin umurnin Mahadi ba. Na rantse, ba zan shagala ga duniyan nan da abin da ke cikinta ba, lahira ita ce gurina. Na rantse, ba zan gudu daga yaki na jihadi ba.” Da haka na rantse, yana jan rantsuwar ina maimaitawa
Ina gama rantsuwa, na’ibi ya mike ya ta da ikama, muka yi salla. Bayan salla, muka yi addu’ar nasara ga Mahadi, sa’an nan ya shiga wa’azi. Ya fada wa jama’a su fid da zukatansu ga abubuwan wannan duniya, su nemi lahira ta kulawa da addini, da shiga jihadi da zuciya daya. Na tabbata duk mutumin da ke wurin ya gaskata Mahadi har cikin zuci, im ba ni da abokan tafiyata ba, watau Sa’id Bey Guma da Dimitri.
Zuwa can bayan mun yi sallar la’asar, sai ya sallame mu muka koma wurin Halifa. Kashegari Halifa ya rarraba mu, kowa aka ba shi ubandaki. Dimitri aka sa shi a hannun wani Greek danuwansa, Sa’id Bey Guma aka kai shi wurin wani Bamisire danuwansa, ni kuwa Halifa ya rike ni na zama yaronsa. Tun daga ran nan na san na tashi a gwamnan kasa, na zama kamamme.
Jumma’a duk za a yi holin mayaka. A kan jeru a yi sahu uku, ko wanne da shugabansu. Bayan an shirya, Mahadi ya kan zo ya tsaya a tsakiya. Sai a ba da odar gaisuwa, mutanen nan dubbai kan dubbai, duk su bude baki gaba daya su gai da Mahadi. Gumjin sai wanda ya ji! Bayan sun yi shiru, sai shi kuma ya shiga kewaya su yana sa musu albarka. A irin wannan farati babu karairayin da soja ba su fada. Wani ka ji ya ce ya ga Annabi a bisa taguwa kusa da Mahadi suna tadi, wani ya ce ya ji murya daga sama tana sa wa sojan Mahadi albarka, tana kuma tabbatar musu da nasara. Wani kuwa sai ya ce ya ga mala’iku suna yi wa Mahadi laima da fikafikansu don kada ya ji zafin rana. Kai, ga su nan dai, maganganu barkatai.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada