HUKUNCIN ZUNUBAN DA MUTUM YAYI LOKACIN DA YAKE DA YARAN TA AJIKIN SA, KAMAR KIN YIN SALLAH

HUKUNCIN ZUNUBAN DA MUTUM YAYI LOKACIN DA YAKE DA YARAN TA AJIKIN SA, KAMAR KIN YIN SALLAH





*TAMBAYA*❓

_Malam ina tambayane akan zunuban da mutum yayi lokacin da yake da yaran ta ajikin sa, kamar : kin yin sallah akan kari, akiyin azahar ko la'asar da gangan sai muce in mukazo kwanciya da daddare zamu rama, ko kuma mukiyin sallah kamar sallah azahar sai muce gobe zamu hada da sallah azahar in gobe🤦🏻‍♀️, ko kuma in muna azumi mucika buta da ruwa mushiga bayan gida musha sai muce zamu rama azumin bayan sallah, amma kuma mukan raman idan akayi sallahn, sai dai fa da gangan muka karyata kuma wlhy locin mun balaga malam don mun fara al'ada shekara 13 ne, to a wannan time inne mukayi ta wannan haukan🤦🏻‍♀️, sai daga baya ne hnkl yana shiga jikin mu, kuma munajin wa'azi akan wasa da sallah da kuma azumi to shine muka daina, to don Allah ya zamuyi da wannan zunuban malam_

_Sai kuma Abu na biyu shine gulman mutane da kuma zagin mutane da dasu rage kudin aikan mutane, in munga abinda yamana kyau na mutum mu dauke bai sani ba, (amma bama daukar kudin da aka ajiye gsky), shima da mukayi tayi lokacin yaran ta🤦🏻‍♀️, Nidai wanda na tuna nayi sadakan su wasu kuma bazan iya tunawa ba, kuma wlhy malam yawanci yanzu haka bamu ma san inda zamu gansu ba balle muneme su yafiya, don Allah shima ya zamuyi da wannan zunuban._

*AMSA*👇

_To Baiwar Allah Duk wanda ya tuba daga zunubi yayi nadama tare da nisantar zunubin to in sha Allahu Allah zai yafe masa, Annabi Muhammadu ﷺ ya fada a cikin hadisi cewa WANDA YA TUBA DAGA AIKATA ZUNUBI YANA KAMAR WANDA BABU ZUNUBINE AGARESHI.(Ibn majah/Darimi)._
.
_Sabida haka sai ku dage da istigfari tare da cika umarnin Allah na ayyuka wajibabbu tare da nisantar ababenda ya haramta ku yawaita ayyukan alkhairi sai su shafe muku laifukanku na baya sabida faďin Allah madaukakin sarki cewa: *Lallai ne ayyukan ƙwarai sunã kõre mũnãnan ayyuka....* (Suratul Hud Aya 114)._
.
_Dangane da hakkokin wadancan mutanan da baki ma san inda zaki gansu ba to sai kiyi sadaka da niyyar ladan yakai zuwa garesu in sha Allahu Allah zai yafe miki_

Wallahu A'alam

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ

*ALLAH TA'ALA YASA MUDACE*

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: 👇_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)