HUKUNCIN WANDA YAYI RANTSUWA BA ZAI SAKE AIKATA SABO BA SAI KUMA YA SAKE AIKATA
*TAMBAYA*❓
MENENE HUKUNCIN WANDA YAYI BAKANCEN BAZAI SAKE AIKATA WANI SABOBA DAYAKE AIKATAWA,SAIKUMA YA AIKATA SABON SHIN ZAYI KAFFARANE?*
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ .
*AMSA*👇
Shi bakance asalinsa makaruhine bai kamata mutum yayi bakance akan wani aikin alkhairi ko sabo ba, Saboda fadin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ( Bakance baya zuwa da alkhairi, kuma yana fitowa daka marowacine) Nisa'i ( 3801) Albani ya ingantashi acikin Sunan Nisa'i.
Shaik Usaimeen rahimahullah yace:
Munaiwa 'yan'uwanmu nasiha akan kada mutum yayi bakance akan dena sabo, dan kada hakan yazamo masa al'ada, tayanda baya iya barin aikin sabo sai inyayi bakance, Allah madaukakin sarki yace:
( ﻭﺃﻗﺴﻤﻮﺍ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﺟﻬﺪ ﺃﻳﻤﺎﻧﻬﻢ ﻟﺌﻦ ﺃﻣﺆﺗﻬﻢ ﻟﻴﺨﺮﺟﻦ ﻗﻞ ﻻ ﺗﻘﺴﻤﻮﺍ ﻃﺎﻋﺔ ﻣﻌﺮﻭﻓﺔ ) ﺍﻟﻨﻮﺭ / 53 .
_Munafukai suna rantsuwa da Allah iyakar rantsuwa idan Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yai musu izinin fita jihadi, zasu fita, Allah yace: Kace dasu kada su rantse akan karya, biyayyarku sananniyace da harshece kawai,.
Kamar hakane ba'a bukatar yin bakance akan daina sabo ko aikin alkhairi, abunda akeso shine kaqulla niyyar mai karfi tadena sabon ko jajircewa wajan aikin alkhairi batare dayin bakanceba, wannan shine abunda yafi alkhairi.
Wanda yai bakance akan bazai kara aikata wani sabo ba sai kuma ya aikata, wajibine yatuba yai istiqfari saboda aikata wannan sabon, dakuma rashin cika wannan bakancen, sannan yayi kaffarar rantsuwa, shine ciyar da miskinai goma, ko tufatar dasu, ko 'yanta baiwa, wadannan abubuwan guda uku cikinsu zai zabi daya yayi, mutum zaiyi wanda yakeso acikinsu, idan bai samu damaba sai kayi azumi guda uku.
Dan haka dolene saikayi kaffarar rantsuwa, sannan kuma saikayi istigfari da tuba akan aikata wannan sabon.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*
