JININ DA YAKE WASA BAYAN AMFANI DA MAGANIN TSARIN IYALI
*TAMBAYA*❓
Menene hukunci akan Jinin-Al'adar da yake yiwa Mace wasa sakamakon tayi amfani da maganin hana daukar ciki? Wato jinin dake fitowa ba alokacinsaba??
:
*AMSA*👇
:
To farkodai dangane da abinda yashafi hukuncin yin Tazarar-Haihuwa shine, akwai Sharuɗɗa guda biyu da'ake buƙata kafin Mace tayi amfani da maganin Tazarar-Haihuwa,
:
→(1)-Sharaɗi na farko shine, ya kasance Mace tana cikin tsanani na buƙatuwar sai tayi hakan, kamar yakasance ƙila bata da cikakkiyar lafiyar da zata iya haihuwa duk Shekara, ko ya kasance 'ya'yan datake haifa basa samun ƙoshin lafiya adalilin hakan, kokuma wata larura dabam wacce take cutar da'ita Uwar kokuma Ɗanta,
:
→(1)-Sharaɗi na biyu shine, dolene ya kasance Mijinta yasani kuma yabata izinin taje tayi,
:
Idan ansamu waɗancan Sharuɗɗa suncika to Shari'a bata Haramta ayi Tazarar-Haihuwa ba, Saidai amma yin Ƙayyade-Iyali wannan kam Haramun Ƙaulan-Wahidan, Sannan yana dakyau kafin Mace tayi amfani da kowanne irin magani na Tazarar-Haihuwa yakasance ita da Mijinta sunje sun nemi shawarar ƙwararren Likita akan hakan saboda yabasu Shawarwari dakuma irin maganin da yafi dacewa da irin yanayin jikin Matar, domin sau dayawa wasu Matan sukanyi amfani da magani kuma aƙarshe abin yacutar dasu, kaga Mace kullum acikin jini take:
:
Alal-Haƙiƙa yin amfani da magungunan hana ɗaukan ciki sukan janyowa Mace matsalokai Dabam-Dabam, kamar rikicewar al'ada, wani lokacin sai Mace taga jinin yazo mata kafin lokacin zuwansa yayi, kokuma taga yayi jinkirin zuwa akan lokacinsa, to amma Malamai sunyi Saɓani agame da hukuncin jinin dake fitowa Mace adalilin amfani da wani magani datayi, Shin wannan jinin shima Jinin-Hailane kokuma Jinin-Cutane?
:
Wasu daga cikin Malaman sukace Mace zata dubane tagani idan jinin yazo da siffane irin ta Jinin-Haila to kawai Jinin-Hailane,
:
Wasu Malaman kuma sukace a'a kawai Mace zataje ta tambayi Likitane idan yacemata Jinin-Hailane to shikenan hukuncin Jinin-Haila yahau kanta kenan,
:
Amma wasu Malaman suna ganin cewa dukkan wani jini da zai fitowa Mace adalilin shan wani magani datayi, sukace to kawai Jinin-Hailane danhaka zata saurarane har ya ɗauke sannan tayi wanka kuma taci gaba da ibadarta, amma idan taga Jinin yawuce kwana (15) bai tsayaba to kawai zatayi wankane taci gaba da ibadarta, domin hukuncin yana ratayuwane dazuwan Jini ko rashin zuwansa, sukace inda Mace zatayi amfani dawani magani wanda zai ɗauke mata zuwan Jinin-Haila natsawon wani lokaci, shikenan tananan amatsayinta na maitsarki, babu yadda za'ayi hukuncin mai al'ada yahau kanta sai in anga jini atare da'ita tukuna, to kamar haka kuma idan Mace tasha wani magani danufin tsaida Haila ko Tazarar-Haihuwa kuma sai al'adarta ta rikice mata, to duk jinin da yazo mata adalilin haka kawai za'abashi hukuncin Jinin-Hailane,
:
Idan kuma yakasance Misali Mace ta saba duk wata tanayin Jinin-Al'ada na kwana biyar, amma bayan tayi amfani da maganin Tazarar-Haihuwa sai Al'adar ta rikice mata, to zata dena Sallah da Azumi harsai wannan jinin yaɗauke, amma idan ya kasance Jinin da yake zuwaɗin yawuce kwana 15 kuma bai tsayaba, to kawai zatayi wankane taci gaba da ibadarta domin yazama Jinin-Istahadha, daga nan kuma hukuncinta zata koma yin amfanine da asalin kwanakin da tasaba tana al'ada acikinsu, idan Misali duk farkon wata ko tsakiyar wata kokuma karshen wata tasaba tanayi Jinin-Al'ada na kwana 5, to da lokacin yayi kawai zata ware waɗannan kwanaki biyar ɗin da tasaba tanayi, bazatayi Sallah da Azumi acikinsuba, idan suka wuce saitayi wanka taci gaba da ibadarta koda jinin bai tsayaba,
:
Ko shakka babu wannan magana tanada ƙarfi sosai awajen Malamai,
:
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:
↓↓↓
:
" ﻓﺘﺎﻭﻱ ﻧﻮﺭ ﻋﻠﻲ ﺍﻟﺪﺭﺏ " ( 1/123 )
:
" ﻓﺘﺎﻭﻱ ﺍﻟﻠﺠﻨﺔ ﺍﻟﺪﺍﺋﻤﺔ " ( 5/402 )
:
" ﻓﺘﺎﻭﻱ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﺔ " ( 2/657 )
Ga mai sha'awar shiga wannan group sai yayi magana ta WhatsApp
08132530316
Bn Ahmad Jigawa
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.*_
https://chat.whatsapp.com/CGmic6azfksGchVijFEZ7e