SALATUL HAAJAH (SALLAR BIYAN BUKATU)



SALATUL HAAJAH (SALLAR BIYAN BUKATU)

TAMBAYA 

Assalamu ya aiki malan Dan Allah inaso kataimaka min da addu'a daxan dunga yi ko sallah ta biyan bukata wlh Ina cin damuwa.


 *AMSA* 👇


Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

In sha Allahu wannan fa'idar Mujarrabah ce. Wato wacce an jarrabah sau da dama kuma anga/ an samu biyan bukata. Kuma tun alokacin Annabi (saww) har zuwa lokacin Sahabbai ana yinta kuma ana ganin saurin biyan bukata. Gata nan kamar haka :

Duk wanda yake da wata bukata awajen Allah, ko kuma wata bukata awajen wani mahaluki, to Kaje wajen Alwala kayi cikakkiyar alwala irin wacce shari'a ta koyar, sannan kaje kayi sallar nafila raka'a biyu a Masallaci ko kuma acikin dakinka.
Kayi Salati ga Manzon Allah (saww) domin shine mabudin kofar shigar addu'a wajen Allah (SWT). Sannan ka daga hannunka kayi wannan addu'ar :
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﺳﺄﻟﻚ ﻭ ﺃﺗﻮﺟﻪ ﺇﻟﻴﻚ ﺑﻨﺒﻴﻨﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻧﺒﻲ ﺍﻟﺮﺣﻤﺔ ﻳﺎﻣﺤﻤﺪ ﺇﻧﻲ ﺃﺗﻮﺟﻪ ﺑﻚ ﺍﻟﻰ ﺭﺑﻲ ﻓﻴﻘﻀﻲ ﺣﺎﺟﺘﻰ .
Allahumma innee As'aluka wa atawajjahu ilaika bi Nabiyyina Muhammadin Nabiyyir Rahmati.
Ya Muhammadu Innee atawajjahu bika ilaa Rabbee Fa yaqdhee haajatee.

FASSARA : Ya Allah ina rokonka kuma ina fuskantowa gareka (wato ina kamun Qafa) da Annabinmu Muhammadu, Annabin Rahama.
Ya (Annabi) Muhammadu! Ni ina fuskantowa da Kai zuwa ga Ubangijina domin ya biya mun bukatata.
Sannan sai ka fadi bukatunka, bayan haka ka Qara yin salati ga Manzon Allah (saww) sannan ka shafa.
Wannan addu'ar tana da ingantaccen asali mai Qarfi acikin Musulunci. Akwai hadisi Sahihi wanda Maluman hadisi masu yawa sun ruwaitoshi ta hanyoyi daban daban daga Sayyiduna Uthman bn Hunaif (rta).
Yace wani Makaho yazo wajen Annabi (saww) yace yayi masa addu'a don samun waraka. Sai Annabi (saww) yace masa idan kaso kayi hakuri. Idan kuma kaso zanyi maka addu'a.
To sai Annabi (saww) ya umurci Makahon cewa ya koma gefe yayi alwala sannan yayi wannan addu'ar.
Uthman bn Hunaif (ra) yace muna zaune awajen sai ga makahon nan ya dawo, idonsa abude ya warke sarai.
Na san wasu zasu ce ai wannan tun lokacin da Annabi (saww) yake duniya ne... Eh hakane. To amma an ci gaba da amfani da wannan fa'idar har bayan Annabi (saww) ya koma ga Ubangijinsa (swt).

GA HUJJAH :
Watarana wani mutum yaje wajen Sayyiduna Uthman bn Affan (ra) alokacin Khalifancinsa, Mutumin yana so yaga Khalifah, amma abun ya gagara. Don haka yazo ya kawo Qara wajen Uthman bn Hunaif (rta) sai shi Bn Hunaif din ya gaya masa wannan fa'idar.
Da yaje yayi, Sai washegari ya tafi Qofar gidan Khalifah, nan take sai ga 'dan aike yazo ya kama hannunsa ya kaishi har wajensa, Kuma ya fadi dukkan abinda yake nema, kuma aka share masa hawayensa.
Don neman Qarin bayani ga wuraren da za'a duba :
# Tarikhul Kabeer na Imamul Bukhariy. juzu'i na 6 shafi na 209, hadisi na 2192.
# Sunanu Ibn Maajah hadisi na 1385. Kuma yace Abu Ishaqa (malaminsa) yace hadisin nan Sahihi ne.
# Al-Jami'us Sahih na Tirmidhiy, Juzu'i na 5 shafi na 569, hadisi na 3578. Kuma yace hadisi ne Mai kyau, ingantacce kuma garibi.
# Musnadu Ahmad juzu'i na 4 shafi na 138 hadisi na 17,246 da na 17,247
# MUSTADRAK na Hakim juzu'i na 1 shafi na 313 da na 519. Kuma yace hadisin Sahihi ne.
# Amalul Yaumi wal Layla na Imamun Nisa'iy, hadisi na 658-659 da kuma 660.
# Musnadu Ibni Humaid juzu'i na daya, shafi na 308 hadisi na 379.
# Dala'ilun Nubuwwah na Imamul Baihaqiy juzu'i na 6 shafi na 166-167.
# Al-Bidayah wan Nihayah na Ibnu Katheer juzu'i na 4 shafi na 558 zuwa na 559.
# Jauharul Munazzam na Imamul Haithamiy shafi na 61.
# Al-Mawahibul Laduniyyah na Qastalaniy juzu'i na 4 shafi na 594.
# At-Targheeb wat Tarheeb na Mundhiriy juzu'i na 1, shafi na 210-211.
Imamush Shaukaniy, bayan ya kawo wannan hadisin kuma ya ingantashi, yayi magana sosai akan halascin yin ita wannan sallar. Aduba cikin littafinsa Tuhfatuz Zakireen shafi na 138.

WALLAHU A'ALAM

Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)